Matar da aka ceto ta koma ruwa domin neman jaririyarta a Maiduguri

..

ASALIN HOTON,BBC/GIFT

Wakilin BBC a birnin Maidugurin jihar Borno ya tattauna da wata mata da suka ceto daga cikin ruwa bayan motarsu ta aiki ta tsaya ta nemi a sauke ta ta koma neman jaririyarta.

Ruwan ya shanye kanta har ma ta fita daga hayyacinta lokacin da tawagar ta ceto ta.

Matar wadda ba a san tun lokacin da take watangaririya a ruwan ba, jim kaɗan bayan dawowa hayyacinta sai ta nemi waɗanda suka ceto ta da su sauke ta.

"Ina jaririyata 'yar wata shida? Ku sauke ni na koma na nemo ta." In ji wannan mata.

Nan take tawagar da ta ceto ta ta ajiye ta domin kada ta faɗo daga motar a lokacin da take tafiya.

Kawo yanzu babu wani bayani dangane da halin da matar ke ciki. Ko ta ga ƴar tata da ta ɓace tun farkon ambaliyar kwanaki biyu da suka gabata?

Maiduguri
Bayanan hoto,Hukumomi da ƙungiyoyin agaji na cigaba da bai wa mutane agaji amma akasari jefa musu kayan ake yi daga saman mota

Halin da mata da ƙananan yara ke ciki a Maiduguri

Maiduguri
Bayanan hoto,Titunan Maiduguri sun ci gaba da kasancewa a cike da ruwa kwana biyu bayan ambaliyar

Labarin baiwar Allah da ta koma neman jaririyarta bayan ta samu an cece ta ɗaya ne cikin labarai marasa ɗaɗin ji da ke faruwa a Maiduguri sakamakon ambaliyar ruwan da ta kassara birnin tun daga ranar Litinin da dare.

Wakilin BBC da ke Maiduguri, Imam Saleh, ya shaida yadda mata da ƙananan yara ke fuskantar manyan matsaloli uku kamar haka:

  • Ɓatan ƙananan yara da mata
  • Rashin lafiya
  • Ƙarancin abinci

Yara da dama sun ɓata

Wasu mata a Maiduguri

ASALIN HOTON,BBC/GIFT

Zuwa yanzu dai babu cikakken bayani dangane da alƙaluman mutanen da aka nema aka rasa sakamakon yadda iyalai suka rabu da juna a yunƙurin tsira da rai.

Sai dai wakilin namu ya ce a ranar Alhamis sun ga mata da ƙananan yara tsundum a ruwa, sannan sun ga gawarwaki na ta yawo a saman ruwan da ke kan tituna.

"Kana iya ganin mata da ƙananan yara tsundum a cikin ruwa suna kuka, wasu tare da mazajensu, wasu ba su san inda suke ba," kamar yadda Imam ya bayyana.

"Akwai matar da na yi magana da ita da ta shaida min cewa kwana biyu kenan ba ta ga mijinta ba sannan ta kasa samun sa a waya. Haka nan, tana fargabar ruwan ya tafi da ɗaya daga cikin ’yaƴanta."

Hukumar ba da agaji ta ƙasa Nema ta tabbatar da mutuwar 37 ranar Laraba.

Matsalar rashin lafiya

Yanzu haka yara da dama na fama da rashin lafiya a sansanonin da suke zaune, kamar yadda wata mata ta shaida wa BBC.

"Yaranmu duk ga su nan a kwance ba su da lafiya. Mun rasa yaya za mu yi."

Hukumar agajin gaggawa ta jihar Borno ta ce tana iya bakin ƙoƙarinta wajen ganin an bai wa marasa lafiya kyakkyawar kulawa.

Sai dai bayanan da BBC ta samu na nuna cewa lamarin ba haka yake ba, kasancewar yanzu abubuwan da gwamnatoci suka fi bai wa muhimmanci su ne tsugunar da mutanen da ambaliyar ta ɗaiɗaita da kuma ba su abinci.

Akwai fargabar da ƙwararru ke nunawa dangane da ƙarin cutukan da ka iya ɓarkewa sakamakon ambaliyar wadda ke cakuɗa da masai da kwatami da ma gawarwakin jama'a da ke yawo a kan ruwa.

'Ana cinye abinci a bar yara da mata'

Wasu mutane da ke cafe kayan agajin da ake jefa musu a Maiduguri

ASALIN HOTON,BBC/GIFT

Bayanan hoto,Wasu mutane da ke cafe kayan agajin da ake jefa musu a Maiduguri

Bayanan da BBC ta tattaro a Maiduguri na nuni da yadda ake raba abinci amma da ƙyar mata da ƙananan yara ke samu sakamakon yawan jama'a, da kuma wawa da masu jini a jika musamman matasa ke yi.

Hotunan da aka ɗauka sun nuna yadda ake jefa wa mutane abinci, inda jama'ar ke wawaso wani abu da ke sa ƙananan yara ba sa samun isasshen abincin.

"Yaranmu da mu muna cikin halin matsala saboda idan aka kawo abincin maza masu ƙarfi ne suke wawashewa tun da kowa na jin yunwa. Mu kuma ba mu da ƙarfin da za mu yi wawaso," In ji wata mata da ke zaune a ɗaya daga cikin sansanonin da aka tanada.

Ta ƙara da cewa "amma lallai gwamnati da jama'ar gari na ƙoƙarin raba abinci, sai dai kuma mu da yaranmu mukan samu abincin ne idan Allah ya sa aka jefo mana kuma ya zo hannunmu".

Wata mai suna Hadiza Jimeh ta ce: "Gaskiya abubuwan da muka fi buƙata su ne abinci da ruwa. Tun da muka zo mu da iyayenmu babu abin da muka ci. Yaranmu sun fi samun matsala. Wani lokacin ne ma idan wani babba ya samu abincin sai ka ƙwace ka bai wa yaronka."

Maiuduguri

Masu lura da al'amura na yi wa al'amarin ambaliyar ruwa a birnin Maiduguri kallon wani ibtila'i daga Allah, wanda ka iya zuwa ba tare da sanarwa ba.

Sai dai wasu na sukar gwamnatoci game da yadda suka gaza ɗaukar mataki duk da cewa tawagar gwamnatin jihar ta kai ziyara Kogin Alau ranar 5 ga watan Satumba, inda ta tabbatar cewa ruwan ya ƙaru, wanda kuma shi ne ya haddasa ambaliyar sakamakon cikar da ya yi.

Masu lura da al'amura da ma waɗanda abin ya shafa na kira ga gwamnatin tarayya da jihohin arewa da kuma masu hannu da shuni su tashi tsaye wajen yi wa matsalar rubdugu kafin jama'a su ƙara tagayyara.