Matan da ke karya dokar saka ɗankwali a Iran na fuskantar ɗauri da ƙwace mota

Shekara biyu bayan mutuwar matashiya Mahsa Amini mai shekara 22 a hannun 'yansanda, da kuma zanga-zangar da ta karaɗe Iran kuma ta ja hankalin duniya, har yanzu mata na cigaba da bijire wa umarnin saka ɗankwali ko kuma hijabi.
Amma yanzu 'yan Hizba sun sake komawa kan titunan ƙasar, sannan kuma akwai sabuwar dokar da za ta hukunta duk wadda ta ƙi bin umarnin saka hijabi.
"Da farko ina ɗan rufe jikina. Sai kuma na fara buɗe maɓallan rigata. Daga baya ma na dinga ɗora mayafi a kaina kawai ba tare da rufe komai ba."
Rojin na ɗaya daga cikin matan da suka daina bin umarnin hukumomin Iran na rufe kai, duk da haɗarin da ke tattare da yin hakan.
Ƙin saka hijabi a waje zai iya jawo cin tara ko kuma ɗauri. Wasu mata sun ƙirƙiri jimlar "bore a kullum" a shafukan sada zumunta domin siffanta abin da suke yi na ƙin bin dokar.
Rojin mai shekara 36 ta ce mata da yawa sun daina tsoron hukunci. A garin Sanandaj da take zaune, ta ce ganin mata ba tare da ɗankwali ba ya zama jiki.
"Za ku sha mamakin ganin yara mata na yawo gashinsu a buɗe," in ji ta.
Mahsa Amini ta mutu bayan 'yan Hizba sun kama ta da zargin karya dokar saka hijabi. A lokacin, shaidu sun ce sun ga 'yansanda na dukanta a cikin mota. Gwamnatin Iran ta musanta cewa ita ce ajalin matashiyar, ta ce matsalar zuciya ce ta kashe ta.
Amma a watan Maris, wata tawagar gano gaskiyar lamari ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce ta gano hujjar azabtarwa a jikinta a lokacin da take hannun 'yan Hizbah, kuma ta ce ta aminta cewa azabtarwar ce ta kai ga mutuwarta.
Mutuwarta ce ta jawo ɓacin rai da ya kai ga zanga-zangar ƙin jinin 'yan Hizba da kuma malaman ƙasar.

Sashen Fasha na BBC ya tattauna da mata 18 a faɗin ƙasar domin fahimtar sauyin da aka samu tun daga lokacin. Mun ɓoye sunayensu don kare su.
Sun amince cewa ba za a taɓa komawa irin wancan lokacin ba kafin mutuwar Mahsa, amma kuma sun bayyana sababbin yunƙurin da 'yansanda ke yi na tilasta wa mata rufe kansu.
Bayan sun ɗan dakata da kewaye a lokacin mutuwar Mahsa, yanzu 'yan Hizbar sun ci gaba da yin hakan a tituna.
Yanzu akan ƙwace duk motar da aka gani da mata cikinta ba tare da ɗankwali ba.
A shekarar da ta gabata, majalisar ƙasar ta amince da wata doka da ta tsawaita ɗauri da kuma ƙara tarar da za a yi wa duk matar da ta karya dokar.
Waɗanda suke yin shigar da "ba ta dace ba" kan fuskanci ɗaurin shekara 10 a gidan yari - inda za a yi shekara uku ana amfani da ita - amma an dakatar da aiwatar da ita saboda ƙin amincewar da zauren magabatan ya yi.

Wasu da yawa da muka yi magana da su sun ce sukan shirya balaguronsu ta yadda ba za a gan su ba.
Wata mai suna Sara K mai shekara 26 daga Mahabad, ta ce: "Wani zubin nakan bi hanyoyin da ba kwalta ba, ko kuma duk titunan da na san akwai kyamara sai na sauko da makari don na ɓoye fuska ta.
"Tsoron da gwamnati ta saka mana a zuci - cewa idan kika fita ba tare da ɗankwali ba za a kama ki, aka tilasta mana saka hannu kan takardun rantsuwar ba za mu karya dokar ba, a ci tararmu, ko a kwace motarmu - ya sa dole mata suke bin dokar."

Tilastawar da ake yi kan saka hijabin ta ƙara jawo rarrabuwar kai game da lamarin baki ɗayansa.
Yayin da wasu mazan ke tausaya wa matan - kamar taimaka musu wajen kauce wa kamun 'yansanda - wasu kan taimaka wa hukumomi wajen tabbatar da dokar.
Shadi mazauniyar Karaj, ta yi imanin cewa an samu ƙarin rashin kwanciyar hankali game da saka ɗankwalin a shekarar da ta gabata.
Ta ce wasu mazan da suka saba goya wa matan baya yanzu kan soki shigar tasu. Shadi ta alaƙanta hakan da dawowar 'yan Hizbah kan tituna, da bijiro da tarar kuɗi, da barazanar rufe duk wani shagon kasuwanci da ke taimaka wa matan wajen saɓa wa dokar.
Sakamakon haka, ta koma saka kayan da za su ba ta damar yin yadda take so ba tare da ta shiga matsala ba.
"Don kauce wa matsala, sai na rataya mayafi a wuyana, duk da cewa ba na ƙaunar hijabin. Ban da gargadin 'yan Hizbar, abin haushi ne duk lokacin da wasu mutane kamar direbobi ko masu shaguna suna yi min magana kan hakan."
Ana yawan samun rahotonnin matan da ake kamawa, a ci tararsu, wani lokacin ma har da duka kan jawo damuwa a zukatan iyaye kan 'ya'yansu mata da ke karya dokar suna sane.
Rojin ta ce: "Kame da cin tarar mata ba mu kaɗai suke shafa ba - takan shafi iyali baki ɗaya. Na ga iyalan da yawa na lallaɓa 'ya'yansu domin su bi dokar idan za su fita waje."
Reza mai shekara 40 kuma lauya a Tehran, ya ce yana sane da wasu ma'aikata da ke yin wasarere da bayanan wasu mata a ɓangaren shari'a.
"Wasu lokutan sai ka ga ma'aikata na ɗaukar lambar wayar wasu mata da zummar taimaka musu amma kuma su fara nuna cewa suna sonsu har sai an kammala shari'ar. Su kuma matan saboda ba su da yadda za su yi, dole su yarda da su don a yi a kammala shari'ar tasu."
Yadda dokar ta samo asali:
- An saka dokar tun daga shekarun 1980
- Iran ta zama jamhuriyar Musulunci bayan juyin juya halin shekarar 1979, lokacin da aka hamɓarar da sarauta kuma malamai suka hau karagar mulkin ƙasar a ƙarƙashin jagorancin Ayatollah Khomeini
- Jim kaɗan bayan haka, ya saka dokar cewa dole ne mata su dinga saka hijabi - ba tare da lura da addininsu ba - sannan aka saka dokoki iri-iri kan motsinsu
- 'Yansandan Musulunci ko kuma Hizba da ake kira "Gasht-e Ershad", su aka ɗora wa alhakin tabbatar da mata sun bi wannan doka
- 'Yan sandan na da damar tsayar da matan domin tantance ko sun rufe kansu, ko duba wando da rigunansu sun yi daidai ko kuma sun ɗame su, ko kuma ma sun caɓa kwalliya sosai
- A 2014, matan Iran suka fara yaɗa hotuna da bidiyonsu a bainar jama'a babu ɗankwali a matsayin wata yekuwa a intanet. Tun daga lokacin wasu ƙungiyoyi suka samu ƙwarin gwiwa, ciki har da "White Wednesdays" da "Girls of Revolution Street"

Yankunan Iran sun bambanta dangane da matsin da matan ke sha.
Sai dai hatta wuraren da suka fi matsawa sun fuskanci sauyi a kwanan nan.
Sanaz daga Mashahad, wani birni da ake zuwa ibada, ta ce a da akwai "tsattsauran yanayi" game da saka ɗankwali, amma tun daga 2022 matan suka fara fita kai a buɗe.