by MUHAMMAD AUWAL UMAR
September 14th 2024.

BBC HAUSA | HUTUN MAULUDI



Gwamnatin Najeriya ta bayar da hutun Maulidi


..

ASALIN HOTON,AJURI NGELALE

Gwamnatin Najeriya ta ayyana ranar Litinin 16 ga watan Satumba, a matsayin ranar hutu ga ma'aikatan ƙasar, domin bikin ranar Maulidi.

Cikin wata sanarwa da babban sakatare a ma'aikatar cikin gida ta ƙasar, Dr. Magdalene Ajani ya fitar, ya ce ministan ma'aikatar, Dakta Olubunmi Tunji-Ojo, ne ya bayyana hutun a madadin gwamnatin tarayya.

Al'ummar musulmai a faɗin duniya na gudanar da bukukuwan Maulidi domin tunawa da zagayowar ranar haihuwar Annabi Muhammad (S.A.W)

''Gwamnati na taya al'ummar musulman ciki da waɗanda ke zaune a ƙetare murnar zagayowar ranar Maulidin'', in ji sanarwar.

Haka kuma ministan ya yi kira ga musulman ƙasar su yi amfani da lokacin bukukuwan wajen yi wa ƙasar addu'ar zaman lafiya da ci gaban ƙasar.

MUKHZAFAYA GLOBAL RAHAMANIYA ENTERPRISES user

MUHAMMAD AUWAL UMAR

[email protected]
WhatsApp Google Map

Safety and Abuse Reporting

Thanks for being awesome!

We appreciate you contacting us. Our support will get back in touch with you soon!

Have a great day!

Are you sure you want to report abuse against this website?

Please note that your query will be processed only if we find it relevant. Rest all requests will be ignored. If you need help with the website, please login to your dashboard and connect to support