'Mun fitar da rai da samun kyakkyawar makoma a Sudan'

Mata

Asalin hoton,Kevin McGregor / BBC

A gefen wani gurɓatattcen titin Adré, wani muhimmin titin da ke kan iyakar Sudan da Chadi, mun iske wata mata mai suna Buthaina mai shekara 38 zaune a ƙasa zagaye da wasu matan.

Kowace daga cikin matan na riƙe da 'ya'yanta. Da alama babu wadda ke da wasu kayayyaki.

Buthaina tare da 'ya'yanta shida sun fice daga el-Fasher - birnin da aka yi wa ƙawanya a yankin Darfur na yammacin ƙasar, mai nisan kilominta fiye da 480 daga inda suke zaune a yanzu - bayan da abinci da ruwan sha ya ƙare musu.

“Komai ya ƙare mana, don haka muka tsira da rayukanmu'', kamar yadda Buthaina ta shaida wa BBC.

“Ba musu muka fita daga garinmu ba, 'ya'yana sun yi nisa a karatu, kuma muna jin dadin rayuwa a gida.

An fara yaƙin basasar Sudan a cikin watan Afrilun shekarar da ta gabata a lokacin da rundunar sojin ƙasar da tsohuwar ƙawarta wato rundunar dakarun RSF suka samu saɓani da juna kan iko.

Yaƙi - wanda bai nuna alamun ƙarewa ba - ya yi sanadiyyar rayukan mutane da dama, tare da raba miliyoyi da muhallansu, sannan ya jefa wasu sassan ƙasar cikin ƙangin yunwa.

A baya-bayan nan ƙungiyoyin agaji sun yi gargaɗin cewar ƙasar ka iya zama mafi fuskanar ƙangin yuwan idan ba a ɗauki matakin agaji ba.

BBC ta fahimci yadda mutanen Sudan ke cikin tsananin buƙatar taimaka a lokacin da muka ziyarci sansannonin da 'yan kasar ke zaune a Adré da ke kan iyakar yammacin ƙasar da kuma jihar Port Sudan, wanda shi ne sansanin bayar da agaji a ƙasar.

Mata

Asalin hoton,Kevin McGregor / BBC

Adré ya kasance wata babar alamar rashin shugabanci da matsalolin jin ƙai da yaƙin ya haddasa.

A watan da ya gabata ne aka buɗe mashigar bayan shafe watanni tana rufe, lamarin da ya sa aka fuskanci ƙarancin motocin kayan tallafi a yankin.

A kowace rana, akan samu gomman 'yan gudun hijirar ƙasar da ke tsallaka kan iyaka zuwa Chadi, mafi yawa daga cikinsu mata goye da ƙananan yaran da ke cike da matsanancin ƙishi.

Suna isa wurin suke nufar tankunan ruwa da Majalisar Dinkin Duniya ta tanadar don ajiye ruwa.

Bayan mun isa Adré, mun garzaya wasu tantuna da aka kafa cike da 'yan gudun hijira a kusa da kan iyakar Chadi.

An yi tantunan da katako da tsoffin tufafi da kuma robobi, wanda kuma ruwan sama ke musu barazana, a yayain da damina ta kankma a yankin.

Mashigin Chadi

Asalin hoton,Kevin McGregor / BBC

An ayyana yunwa - a sansanin Zamzam na yankin Darfur - sakamako kasancewarsa ɗaya daga cikin wuraren da yaƙin ya fi yi wa illa.

Hukumar Abinci ta Majalisar Dinkin Duniya, WFP ta ce ta kai tan 200,000 na abincin tsakani watan Afrilun 2023 zuwa Yulin 2024, sai dai bai kai abin da ake buƙata ba.

An dai zargi ɓangarorin da ke yaƙi da junan da hana shigar da abinci zuwa yankunan da ke ƙarƙashin ikonsu.

An zargi RSF da sauran ƙungiyoyin mayaƙa da sacewa tare da lalata kayan agajin, yayin da aka zargi sojojin ƙasar da hana kai agaji yankunan da RSF ke iko da su, ciki har da yankin Darfur.

BBC ta tuntuɓi duka ɓangarorin biyu, kan waɗannan zage-zarge, to amma ba su ce komai ba, kodayake a baya sun sha musanta zarge-zargen.

Motar agaji guda kan jira aƙalla mako shida ko fiye a Port Sudan kafin sojojin ƙasar su ba ta damar wucewa don kai agajin.

A lokacin da muka ziyarci Port Sudan mun ziyarci wani sansani da mutanen da suka rasa muhalansu ke zaune.

A tsakanin tantuna da ke wurin, mun ji labarai masu yawa na tayar da hankali.

A wani tantin mun samu gungun wasu mata zaune, wasu daga cikinsu riƙe da jarirai, dukkan sun bayar da labarin cin zarafinsu da fyaɗe da azabtarwa a gidajen yarin RSF.

Ɗaya daga cikin matan da BBC ta zanta da su ta ce an kama ta tare da ɗanta mai shekara biyu, aka kuma kai ta Omdurman, kusa da Khartoum, babban birnin ƙasar.

“A kowace rana sukan fitar da ɗana daga ɗakin da suka ajiye ni, kuma ina jin kukansa a lokacin da suke yin min fyaɗe'', kamar yadda ta shaida wa BBC.

“Hakan ya faru da ni babu adadi nakan ɓarke da kuka a duk lokacin da na ji shi yana kuka.”

Mata

Asalin hoton,Kevin McGregor / BBC

Haka kuma a sansanin, mun tarar da wata mata mai suna Safaa, wata uwa mai 'ya'ya shida wadda ta tsere daga Omdurman.

Da muka tambaye ta inda mijinta yake, sai ta ce baya tare da su, saboda dakarun RSF ne nemansa ruwa a jallo sakamakon yunƙurin guduwa da ya taɓa yi.

“A kowace rana 'ya'yana kan tambaye ni ''Ina babanmu? Yaushe zai zo? Amma tun watan Janairu ban sake ji daga gare shi ba, ban ma sani ba ko yana raye ko ya mutu'', in ji shi.

Da aka tambaye ta wace makoma take hangowa kanta da kuma yaranta, sai ta ce wace makoma? ai ba mu da wata makoma - babu abin da ya rage mana. An cutar da yara na.

“A kowace rana, ɗana mai shekara 10 na kukan komawa gida. Mun fito daga gidanmu mai kyau, yara suna zuwa makaranta, amma yanzu mun koma rayuwa a tanti.''

BBC ta tuntuɓi RSF don jin ta baƙinta kan zargin fyaɗe da sauran laifukan cin zarafi da ake yi wa mayaƙansu, amma ba ta ce komai ba. To amma a baya ta sha musanta irin waɗannan zarge-zarge.

Mataimakshiyar shugaban MDD

Asalin hoton,Kevin McGregor / BBC

BBC ta ziyarci Adré da Port Sudan ne tare da mataimakiyar shugaban Majalisar dinkin Duniya, Amina Mohamed da tawagarta, wɗanda suka ziyarci jami'an gwamnatin Sudan da kuma mulkin sojin ƙasar, Abdel Fattah al-Burhan, domin nema

Manufarta shi ne mayar da batun yaƙin Sudan kan ajandar duniya, a daidai lokacin da hankalin duniya ya karkata kan yaƙin Gaza da na Ukraine.

“Idan duniya ba ta mayar da hankali kan Sudan tare da ɗaukar matakai ba, to mutane da dama za su mutu.” in ji ta