KYAWAWAN YABO GA SAYYIDINA MUHAMMADU RASULULLAHI SALLALLAHU ALAIHI WA'ALAA AALIHI WASSALLAM ☑️
✓ Yafi kowa sanin ya kamata da tafi da komai dai-dai ba tare da kuskure ba, ga shi ƙwararre a kowanne fanni, babu abinda zaiyi wani yace da haka yayi da yafi a'a duk abinda yayi shine yafi. Ba'a taɓa jin sa ya zagi kowa ba kuma duk irin cutar da za'amasa baya taɓa ramawa da cuta sai dai da alkhairi. Yana da cikar kunya da cikar tawadhi'u (Ƙan-ƙan da kai) saboda tsabar kunyar sa ne ya sa bai taɓa taɓa hannun wata macen da ba tashi ba duk da kasancewar komai nasa ne sallallahu alaihi Wasallam.
Yana haƙura da abinda yake halalin sa ne ya ƙi wa kansa saboda ya samar da daidaito a cikin mu. Baya taɓa barin abinda zai cutar da mu ya same mu sai ya kare mu daga shi sallallahu alaihi Wasallam.
Har wata rana Nana A'ishah taji Annabi yana yi mata addu'a da tayi masa magana sai yace babu ranar da zata wuce face sai yayi mana irin wannan addu'ar kuma bai taɓa faɗawa kowa ba. Duk da Allah ya faɗa da bakin sa na kudra cewar bai saukar masa da wahayi dan ya wahala ba amma haka yake haƙura da wannan banonzar da Allah yayi masa ya dinga bautar Allah ba dare ba rana. Shi ba laifi yake yi ba amma yafi Kowannen mai aikata laifi ibada da tsoron Allah Sallallahu alaihi Wasallam.
Duk daɗewar da yake a cikin sujuda amma goshin sa bai taɓa nuna alamar wahala ba ko kuma guyawun sa da ƙafar sa da duk sauran jikin sa ba sallallahu alaihi Wasallam.
Allah ya ƙarawa Manzon Allah Daraja. Allah ya barmu a nasa duk rintsi duk wuya Amin.
Khamis Na Annabi
08026407773
((LA'UZRA SOCIAL MEDIA 🎥))