Aikin da-na-sani - Matar da tiyatar ƙara tsawo ta zame mata alaƙaƙai

- Tom Brada
- BBC News
Gargadi: Wannan makalar na dauke da bayanan da suka shafi lafiya, wadanda za su iya tayar da hankalin mai karatu.
Kafafun Elaine dauke suke da wasu lafta-laftan tabbunan ciwo masu launin makuba, kowacce daga cikin kafafun na tuna ma ta da tiyatar kara tsawon kafar da aka yi ma ta, sai dai haka ba ta cimma ruwa ba.
Tun dai shekarar 2016, aka yi wa matar mai shekara 49 tiyata sau biyar, da gyaran kashin kafa sau uku. Duk abin da ta tara ya tafi a asibiti, lamarin da ya sa ta maka likitan da ya yi mata tiyatar gaban shari'a, daga bisani a watan Yuli aka daidaita, sai dai babu biyan bukata.
Akwai lokacin da aka sanya wa kafar Elaine karfe cikin kashi, akwai lokacin da ta ce ta na jin kamar ana gasa kafar daga cikin tsokarta.
“Na ga ta kaina, garin neman gira na rasa ido, amma duk da haka na kubuta,” in ji ta.
Likitanta ya sha musanta sakaci ne ya haddasa hakan, ya kare matakin da cewa, daman tun kafin lokacin tiyatar an garhade ta kan matsalolin da za ta iya fuskanta.

Dama can Elaine ta tsani tsawonta.
"Lokacin da ina 'yar shekara 12, doguwa ce ni, na fi yawancin 'yan mata tsawo. Amma ina kai wa shekara 14 sai na fara gajarcewa, na zama 'yar guntuwa. Sannu a hankali sai na fara tsanar kaina, ana kallon duk mai tsawo a matsayin kyakkyawa. Sai zuciyata ta kitsa min dogayen mutane sun fi samun damarmaki a rayuwa."
Kafin ta karasa girma, damuwar ta zama doguwa ya girmama.
Elaine ta yi amannar cewa tana da wata cuta da ke hana ta girma, wata cuta da ke damun kwakwalwar mutane, inda mutum zai dinga kushe duk halittarsa, ko da mutane ba su yi magana a kai ba. Lamari ne da ke sanya mutane zautuwa saboda damuwa.
Lokacin da Eliane ta kai shekara 25, sai ta yi kicibis da wata makala da aka rubuta kan wani asibitin 'yan China, inda mutane suke zuwa ayi musu tiyata a kafa, inda ake kara wa kashin kafar tasu tsawo. Makalar na dauke da bayanai da hotunan kafafun da aka karawa tsawo, amma wasu ba su yi nasara ba, sun kamu da cutuka masu wuyar sha'ani.
Lamari ne mai tayar da hankali, amma duk da haka, Elaine ta yi shahadar kuda.
"Na san mutane za su dasa ayar tambaya kan ingancin aikin. Amma idan ka na fama da matsalar da ta shafi ingancin jikinka, babu wani bayanin da za a yi maka da zai sauya maka tunani a kan abin da ka kuduri niyya," in ji Elaine.
Shekaru 16 bayan nan, sai Elaine ta gano wani asibiti mai zaman kansa, wanda ke aikin tiyatar kara tsawo a birnin Landan. Kwararren likitan kashi Jean-Marc Guichet, ya kware wajen kara tsawon kashi, wanda ya kirkiri injin da yake amfani da shi mai suna Guichet Nail.
“Lamari ne mai faranta rai a gare ni, saboda zan iya yin tiyatar a Landan, kasancewa zan yi jinya a gida,” in ji Elaine.
“Dr Guichet ya bayyana min yadda aikin ya ke da kuma yiwuwar samun matsala. Ya fada min zan iya samu ciwuka a jijiya, da toshewar jini, da yiwuwar kasusuwan ba lallai su koma yadda suke ba.
“Amma saboda na yi nawa binciken, sai na ga ai wurin likita mai tsadar gaske na zo, don haka zan samu biyan bukata. Mafarkina shi ne na kara tsawo zuwa kafa biyar.”
Ranar 25 ga watan Yuli, Elaine ta biya zunzurutun kudi fam 50,000 domin yin tiyatar, ta kuma kudurta a ranta lallai rayuwarta za ta sauya.
Aikin tiyatar kara tsawo dai ba abu ne da aka saba da shi ba, amma asibitocin kudi masu zaman kansu a sassa daban-daban na duniya na yin aikin. Ya danganta da inda mutum yake zaune, amma dai kudin tiyatar na farawa ne daga fam 15,000 zuwa fam 150,000.

“Cike nake da zakwadi lokacin da na farka, saboda abin kamar a mafarki nake ji. Amma minituna 90 bayan tiyatar, sai na fara jin ciwo. Ai sai na fara jin kamar ana dafa min kafafu. Kamar an hasa wuta a can cikin kashina. Ai daren nan baki daya kwana na yi ina ihu da kururuwa har karfe 6 na safe.”
Daman tiyata irin wannan kan zama haka bayan mutum ya farfado, dole zai ji ciwo. Saboda ana karya kashin ne a lokacin tiyatar sai a sanya rodi tsakanin kashin da aka karya, girman rodin ya danganta da tsawon da mutum ke so.
A hankali ake kara tsawon rodin domin cimma abin da ake bukata, amma fa tsakanin kashin kafar nan da aka karya. Ana sa ran a hankali kashin zai warke tare da hadewa da dan‘uwansa, domin cike gibin da aka bude saboda sanya karfen rodi.
Tiyatar na da sarkakiya sosai.
“Tiyatar kara tsawon na daukar akalla watanni biyu zuwa uku, daga nan kuma za a dauki watanni hudu zuwa shida kafin mutum ya warware ya koma daidai,”kamar yadda farfesa Hamish Simpson,tsohon mamba a kungiyar likitocin kashi ta Birtaniya ya yi gargadi. Ya kara da cewa yawancin mutane, za su iya daukar shekara guda ko fiye da hakan kafin su warke.
Bayan an gama tiyatar, sai aka fara shirin kara tsawon kafar Elaine. Kusan kowacce rana sai an yi wani abu da zai sanya ta shiga wani yanayi, misali sauyawa da jujjuyawa kamar ya na sanya karfen rodin da ke kafar ya fara yi ma ta ciwo. Wannan ne yanayin da ke sanya kusoshin da ke jiki motsawa su kuma sanya kafar yin tsawo a hankali. Amma makonni biyu bayan nan, sai ta fara shiga wani bala'in.
“Sai in dinga jin tsananin ciwo a kafafuna. Da daddare kuma idan ina dan juya a gado, sai na dinga jin karar kamar karafuna su na gogar juna, daga nan sai azabar ciwo.”

Elaine ta je asibiti domin yin hoton kashi, wannan ya tabbatar da tsoron da ta ke ji. Kusar da ke kafar hagu ce ta karye, kuma ta karye ne daga kashin da ya fi kowanne inganci da karfi a jikin dan‘adam. Hankalin ta ya yi mugun tashi, amma sai Dakta Guichet, ya karfafa ma ta gwiwa.
“Ya shaida min kar na damu, babu abin da zai faru. Ki jira ya warke, da zarar ya warke za mu sake fara aikin.”
Za su ci gaba da aikin kara tsawon kafar Elaine ta dama, yayin da za su tsawaita lokacin da za a yi ta kafar hagu, wadda za a kara tsawonta kamar yadda ta kafar dama ta ke.
Elaine ta ce an shaida ma ta karin tiyatar da za a yi mata da za ta biya dubban fama-famai, amma ba ta damu ba ta ce za ta biya, in dai bukatarta za ta biya.
Zuwa watan Satumba, tsawon kafarta ta dama ya karu da santimitia 7, sai dai lamarin akwai tsoratarwa. Babanbancin tsawon kafafun biyu na haddasa matsaloli, inda ya sanya kashin bayanta lankwashewa, da tsananin ciwo.

Bayan makwanni shida, hoton kashin Elaine da aka yi ya nuna kafar dama ta na da matsala, saboda kashin ba ya tsirowa, kuma bai hadu da rodin da ke tsakaninsu ba.
Elaine ta garzaya wurin Dr Guichet domin ya taimake ta, wanda ya kara sanya lokacin yin wata tiyatar a wani asibiti da ke birnin Milan inda can ma yake yin aiki. A ranar 1 ga watan Afirilu 2017, aka fara yi ma ta wata tiyatar ta kara tsawon kafar hagu, aka kuma fara yi mata allurar bargo a kafar dama, domin taimakawa kashin tsirowa da wuri.
“Dr Guichet ya shaida min cewa kusar ta karye, a lokacin da ya ke ciro ta,'' in ji ta. “Ya na da wata kusar ta wani maras lafiya, don haka sai ya sanya min ita.” Ta kara da cewa, hakan na nufin za ta kara kashe wasu kudaden.
Kwanaki uku bayan nan, ta gagara ko da motsa kafarta, amma ta zaku ta koma gida, haka Elaine ta koma birnin Landan. Ta ce da fari su na yawan magana da Dr Guichet akai-akai, amma zuwa wani lokaci wannan kyakkyawar alakar tsakanin likita da maras lafiya ta kau tsakaninsu.

Elaine ta rasa tudun dafawa, a watan Yulin 2017 ta yi kokarin ganin likitan kashi a hukumar inshorar lafiya ta Birtaniya wato NHS.
Ta ce ga abin da likitan ya fada mata "Wannan ba lamari ne mai sauki ba."
"Zan dauki akalla shekara biyar kafin na warke baki daya," in ji shi.
Bayan shekara 8 da yin ainahin tiyatar kara tsawon, Elaine ta ce har zuwa lokacin ba ta warke ba, ta samu matsaloli da dama na lafiya.
“Daga shekarar 2017 zuwa 2020, sai da na boye kaina daga mutane. Ba ni da miji bare mashinshini, ba ni da aiki, ba ni da ko taro, ga kuma nakasa.”
Amma a baya-bayan nan ta fara samun sassauci. Bayan shafe shekaru hufu su na tafka shari'a, daga baya Dr Guichet ya amince ya biya Elaine wasu kudade, domin sasantawa da kawo karshen zargin da take masa, cewa shi ne ya sanya ta halin da ta samu kan ta a ciki.
Lauyan likitan fidar, ya ce sam babu laifin wanda ya ke karewa, kuma babu sakacin Dr Guichet, ya shaida wa kotu cewa: “Dr Guichet bai yi sakaci kan aikin tiyatar nan ba, abin da ya faru da mis Elaine ba mai dadi ba ne, to amma wanda na ke karewa ya shaida ma ta tun kafin aikin tiyatar, irin abubuwan da za su iya faruwa, amma ta ce ta ji ta gani.
Ina laifin Dr Guichet a nan? Sannan matsalar da aka samu ta hadewar kashin kafar hagu, Mis Elaine ce ta janyo saboda ta na shan magungunan cutar tsananin damuwa, wanda ba ta fada wa likitanta hakan ba kafin a yi tiyatar, sannan ita ce da gangan ta kara tsawon kafar alhalin ga yadda aka yi yarjejeniya da ita”
Elaine kawai ta dauka komai lafiya tun da ai ta na kashe makudan kudade. Sai dai abin da ya biyo baya ba mai dadi ba ne, fannin kashe kudi da rashin biyan bukata.
“Na yi asarar lokacina, da shekaru masu matukar muhimmanci a rayuwata. Na san mutane da dama za su so jin na ce ina da-na-sanin abin da ya faru, ko idan aka tambaye ni da kin san haka za ta faru za ki yi tiyatar? Abin da zan fada masu shi ne a'a ba zan taba yi ba, na gode kwarai’.”