Matakan da za ku ɗauka idan mutum ya ci abinci mai guba

Abincin gayya

ASALIN HOTON,GETTY IMAGES

A baya-bayan nan labarin mace-macen mutane sanadiyyar cin abinci mai guba ya tayar da hankalin al'umma, musamman a jihohin arewacin Najeriya.

Cikin wata ɗaya an samu rahoton mutuwar kimanin mutum 24 a jihohin Sokoto da Zamfara, inda lamarin ya shafi iyalai guda uku.

Hakan na zuwa ne yayin da rahotanni ke cewa mutane na komawa cin ganyayayyaki da ba su saba amfani da su ba sanadiyyar matsin tattalin arziƙi.

Mace-macen sun fara tayar da hankali ne bayan wasu iyalai su shida sun rasa rayukansu a jihar Sokoto bayan cin abinci da aka haɗa da rogo.

Sai kuma wasu mutum shida ƴan gida ɗaya da suka mutu sakamakon shan miya mai ɗauke da gishirin lalle ko gishirin ƙunshi.

Mutanen da suka mutu sun haɗa da matar gidan da kuma ƴaƴanta biyar.

A wani labarin mai kama da irin wannan, mutum 12 ne suka mutu a garin Ɗaki Takwas da ke Ƙaramar Hukumar Anka a Jihar Zamfara, bayan sun sha miyar ganyen lalo mai ɗauke da sinadarin maganin kashe ƙwari.

Mutum 25 ne da suka fito daga gidaje biyu suka sha miyar a ranar Juma'a, inda tun a lokacin suka fara rasuwa ɗaya bayan ɗaya.

Shugaban Hukumar kula da lafiyar al'umma ta jihar Zamfara, Yusuf Abubakar ya bayyana wa BBC cewa: “Manomi ne ya je ya yi feshin ƙwari da wasu ganyayyaki da ya ba ya so, daga ciki akwai ganyen lalo, wanda ana miya da shi a gidajenmu na Hausawa.

"Ya yi feshin da safe, su kuma suka je da rana domin nemo ganyen da za su yi miya. Daga bisani sai suka kamu da amai da gudawa da zubar da yawu. Daga nan ne aka ɗauke su zuwa asibiti, inda ma’aikatan lafiya suka zo domin ba su kula ta gaggawa."

Jami’in ya ce kasancewar wasu sun fi wasu shan miyar, sai ya kasance wasu sun mutu a gida, wasu suka mutu a wani asibiti a Anka, wasu kuma sai da aka kawo Babban Asibitin Taryya da ke cikin Zamfara suka ce ga garinku."

Yadda ake gane mutum ya ci abinci mai guba

Dokta Fatima Adamu, likita a Asibitin Koyarwa na Aminu Kano, ta ce, "Gaskiya alamomin ba wai muna gane su da iɗo ba ne, yawanci idan aka kawo ka asibiti, akwai wasu tambayoyi da muke yi, da amsoshin ne za mu gane gubar ce ko wani ciwon daban.

Amma ta bayyana wasu alamomi da suke gani a tattare da waɗanda suka ci guba, alamomin sun haɗa da:

  • Amai
  • Ciwon ciki
  • Zazzaɓi

A cewar dokta Fatima daga wannan lokacin ne akan binciki mutum game da abin da ya ci da kuma ko akwai wasu da suka ci abincin bayan shi.

Dokta Fatima ta ƙara da cewa ba dole sai an jira an ga kumfa na fitowa daga bakin mutum ba, domin a cewarta, gubar ma kala-kala ce.

Abin da ke faruwa a jikin mutum idan ya ci abinci mai guba

..

ASALIN HOTON,GETTY IMAGES

Dokta Fatima ta cewa ana samun matsala ne da zarar gubar da mutum ya ci a cikin abinci ta shiga jikinsa.

“Jikin zai gane baƙon abu ya shigo. Jiki kuma yana da nasa kariyar, idan kariyar ta yi ƙoƙarin yaƙi da baƙon, ta gaza, sai ya fara nunawa a jikin mutum. Wata gubar ba ta buƙatar magani.

Za a zai iya warkewa bayan cin abinci mai guba?

"Bayan wasu kwanaki za ta warke, wasu ne suke buƙatar magani. Ya danganta da yanayin garkuwar jikinka da kuma ƙarfin gubar.”

Sai dai Doktar ta ce bai kamata a tsaya a gida ba idan ana tunanin an ci abinci mai guba, inda ta ce ya fi kyau a yi gaggawar tafiya asibiti.

“kowane guba akwai irin abin da za a yi, wani wanke masa abin da ya ci ɗin za a yi, wani kuma za a ba shi magani ne, sai ya hana abin da ya ci ɗin shiga cikin jininsa, sai ya yi bayan-gida, wani kuma maganin zazzaɓi kawai za a ba shi.”

Ta ƙara da cewa a daina tsaya ɗaukar matakai a gida, inda ta ce hakan ya jawo wasu matsalolin har ake rasa rai ma.

Kurakuran da ake yi idan mutum ya ci abinci mai guba

Dokta Fatima ta ce akwai wasu abubuwa da mutane ke yi da sunan sauƙaƙa tasirin guba a jikin ɗan'adam, waɗanda a kimiyyance kuskure ne kuma za su iya yin illa ga mutum.

Ta ce: “Za ka ji misali ana cewa a ba mutum madara ko wani abun, ko kuma ka ji ana cewa mutum ya yi yunƙurin amai. To idan sinadarai ne ko irin acid haka, idan aka ce mutum ya yi amai, ƙara illata shi za a yi, ko kuma idan aman ya bi ta wajen numfashinsa, zai iya jawo wa ya rasa ransa.

Don haka irin waɗannan abubuwa babu amfani a jira, da zarar an ga alama a yi gaggawar kai mutum asibiti kawai.”

Hanyoyin guje wa cin abinci mai guba

..

ASALIN HOTON,GETTY IMAGES

Guba dai na yin illa ga mutum ne idan ta shiga jiki, ta yaya mutum zai iya hana kansa cin abinci mai gubar?

Liktar ta ce akwai wasu muhimman matakan da suka kamata a ɗauka domin guje wa cin guba a cikin abinci:

  • Tsaftace abincin
  • Tsaftace wurin girki
  • Adana abinci a wuri mai kyau inda wani abu ba zai gurɓata shi ba
  • Amfani da ruwa mai tsafta
  • Amfani da kwanukan cin abinci masu tsafta
  • Adana abinci cikin firji
  • Wanken hannu a kowane lokaci
  • A daina ajiye abubuwa masu guba kusa da wurin girki