Iko, arziki, ƙasaita: Abubuwan da suka sa yarima mai jiran gadon Saudiyya Mohammed bin Salman ya gawurta

- Jonathan Rugman
- Ɗanjarida kuma marubuci
A watan Janairun 2015, Abdullah, sarkin Saudiyya mai shekara 90, na gadon mutuwarsa a asibiti. Ɗan'uwansa Salman na shirin zama sarki - shi kuma ɗan da Salman ya fi ƙauna, Mohammed, na ɗaura ɗamarar kama mulki.
Yariman wanda aka fi sani da laƙabin MBS kuma mai shekara 29 a lokacin, na da buri sosai a kan ƙasarsa, mafi girma a tarihinta; amma yana fargabar wasu daga cikin 'yan'uwansa a masarautar za su iya kawo masa tsaiko.
Saboda haka da tsakar wani dare a wannan watan, sai ya gayyato babban shugaban fannin tsaron ƙasar zuwa fada domin neman goyon bayansa.
An faɗa wa Saad al-Jabri cewa ya bar wayarsa a kan wani teburi a waje. Shi ma MBS ya yi hakan. Sai mutanen ska zama su biyu kawai. Matashin yariman na ɗari-ɗari da 'yan leƙen asirin fadar, abin da ya sa ya tsinke wayar tarho ɗaya tilo da ke ɗakin.
A cewar Jabri, MBS ya yi magana kan yadda yake son ya tayar da ƙasar daga barcin da take yi da zimmar mayar da ita kan ganiya a tsakanin ƙasashen duniya. Idan ya sayar da hannun jari a kamfanin mai na gwamnatin ƙasar Aramco - mafi girma wajen samun riba a duniya - zai ɗauke dogaron da ƙasar ta yi kan man fetur kacokam. Zai zuba biliyoyin dala na hannun jari a kamfanonin fasahar Amurka (Silicon Valley) da suka haɗa da kamfanonin tasi na zamani kamar Uber. Sannan idan ya bai wa matan ƙasar 'yancin shiga aikin gwamnati, zai iya ƙirƙirar aikin yi har miliyan shida.
Cikin mamaki, Jabri ya tambayi MBS irin zaƙuwarsa kan wannan buri. "Ka taɓa jin labarin Alexander the Great?”
Sai MBS ya dakatar da hirar daga nana. Ganawar da aka tsara za a yi ta cikin minti 30 ta zarce zuwa awa uku. Jabri ya tarar da kiraye-kiraye a wayarsa masu yawa daga manyan jami'an gwamnati bayan ya fita daga ɗakin, inda suke ta fargabar inda ya shiga.
A shekarar da ta gabata, tawagarmu ta yi ta jin ta bakin abokai da kuma masu adawa da MBS a Saudiyya, da kuma masu leƙen asiri na ƙasashen Yamma da jami'an difilomasiyya. BBC ta bai wa gwamnatin Saudiyya damar mayar da martani game da zarge-zargen, sai dai ta zaɓi ta yi gum da bakinta.
Saad al-Jabri ya kai ƙololuwa a ɓangaren tsaron Saudiyya ta yadda har ya ƙulla abota da shugabannin hukumomin leƙen asiri na Amurka (CIA) da Birtaniya (MI6). Yayin da gwamnatin Saudiyya ke kallon Jabri a matsayin korarre, yana cikin mutanen da suka kowa tsaurin idon adawa da yadda MBS ke mulkin Saudiyya a fili - kuma abubuwan da ya faɗa mana a wannan hirar na da ban mamaki.
Ta hanyar tattaunawa da mutanen da suka san MBS, mun yi ƙarin haske kan abubuwan da suka sa MBS ɗin ya gawurta - ciki har da kisan ɗanjarida Jamal Khashoggi a 2018, da kuma ƙaddamar da yaƙi a Yemen.
Yayin da mahaifinsa ke ƙara tsufa, yariman mai shekara 38 a yanzu shi ne shugaba a fakaice a ƙasar da aka saukar da Musulunci kuma wadda ta fi kowacce arzikin man fetur a duniya.
Ya fara aiwatar da sauye-sauyen da ya faɗa wa Saad al-Jabri - yayin da kuma ake zargin sa da take haƙƙin ɗan'adam ta hanyar murƙushe 'yancin faɗar ra'ayi, yin amfani da hukuncin kisa da yawa, da kuma ɗaure mata 'yan fafutika.
Mafarin sauyi mai kamar wuya
Sarkin farko a Saudiyya ya haifi 42, cikinsu har da Salman mahaifin MBS. Akasari waɗannan 'ya'yan ne ke gadar kujerar. Sai a lokacin da biyu daga cikinsu suka mutu a 2011 da 2012 aka ɗago Salman zuwa matakin mai jiran gado.
Masu leƙen asiri na ƙasashen Yamma sun lazimta wa kan su nazari kan masarutar Saudiyya kamar yadda suke yi wa gwamnatin Rasha - su yi ta nazari kan wane ne sarki na gaba. A wannan mataki, MBS ya yi ƙanƙanta sosai ta yadda ba su ma saka shi cikin masu jiran gadon.
"Babu wanda ya san shi lokacin yarinta," a cewar Sir John Sawers, shugaban MI6 zuwa 2014. "Ba a saka shi cikin waɗanda za su yi mulki."

Haka nan, yariman ya girma a fadar da ba a fiya hukunta masu rashin tarbiyya ba, kuma hakan zai iya zama dalilin da ya sa ba shi lura sosai game da abin da wasu matakan da yake ɗauka za su jawo har sai ya ƙaddamar da su.
MBS ya fara gawurta ne a birnin Riyadh tun yana ɗan shekara goma sha kaɗan, lokacin da aka yi masa laƙabi da "Abu Rasasa" ko kuma "Uban Harsashi", bayan an zarge shi da aika wa wani alƙali harsashi sakamakon hukuncin da ya yanke da bai ba shi nasara ba a wata shari'ar muhalli.
"Yana da ɗan rashin tausayi," in ji Sir John Sawers. "Ba shi bari a ɗaga masa yatsa. Amma hakan ya sa ya iya kawo wasu sauye-sauye da babu wanda ya iya yin hakan."
Daga cikin sauye-sauyen da aka yi maraba da su, a cewar shugaban na MI6, shi ne katse kuɗaɗen da Saudiyya ke bai wa masallatai a ƙasashe da makarantun Islamiyya waɗanda ke ƙyanƙyasar masu tsattsauran ra'ayi - abin da ƙasashen Yamma ke gani a matsayin tsira gare su.
Mahaifiyar MBS mai suna Fahda 'yar asalin Larabawan ƙauye ce kuma ana kallon ta a matsayin wadda mahaifinsa ya fi so cikin huɗu da yake da su. Jami'ai a ƙasashen Yamma na ganin sarkin ya sha fama da cutar mantuwa tsawon shekaru kuma MBS ne wanda ke yawan taimaka masa.
Jami'an difilomasiyya da yawa sun faɗa mana yadda suka gana da sarkin tare da ɗansa MBS. Yariman ne ke rubuta abubuwa a wayarsa, sannan ya aika su zuwa wayar mahaifinsa da zimmar tunasar da shi abin da zai faɗa a gaba.
"Na zaci MBS na faɗa masa abin da shi yake so ya faɗa ne," a cewar Kim Darroch, mai bai wa tsohon Firaministan Birtaniya David Cameron shawara kan tsaro.
Yariman ya ƙagu sosai mahaifinsa ya zama sarki, inda har ma a 2014 aka yi zargin cewa ya ba da shawarar a kashe sarkin lokacin Abdullah - kawunsa - ta hanyar saka masa guba a zobe da aka samo daga Rasha.
"Ban sani ba ko kuri kawai yake yi, amma dai mun ɗauki lamarin da gaske," in ji Jabri. Tsohon jami'in tsaron ya ce ya ga wani bidiyon sirri da aka naɗa na MBS yana magana a kan yin hakan. "An hana si shiga fada, aka hana shi gaisawa da sarkin na tsawon wani lokaci."
Baya sarkin ya rasu da ikon Allah, ɗan'uwansa Salman ya karɓi ragama a 2015. A lokacin ne kuma aka naɗa MBS ministan tsaro, wanda bai yi wata-wata ba wajen ƙaddamar da yaƙi.
Yaƙi a Yemen
Wata biyu bayan haka, yariman ya jagoranci wani ƙawancen ƙasashe yankin Golf domin yaƙar ƙungiyar Houthi wadda ta ƙwace mulki a yammacin Yemen, kuma MBS na ganin ƙungiyar wakikiya ce ta babbar abokiyar adawar ƙasarsa wato Iran. Yaƙin ya haifar da mummunar ɓarna.
"Babu dabara a matakin," in ji Sir John Jenkins, tsohon jakadan Birtaniya a Saudiyya kafin fara yaƙin. "Wani babban jami'in sojin Amurka ya faɗa mani cewa saura awa 12 kafin ƙaddamar da yaƙin aka sanar da su, abin da ba a saba gani ba."
Yaƙin ya taimaka wajen sauya kallon da ake yi wa yariman da ba a san shi ba sosai zuwa gwarzo. Sai dai kuma, shi ne abu na farko da hatta abokansa ke gani a matsayin kuskure.
Sai kuma ga wani salon shugabanci na MBS: aniyarsa ta jefar da tsarin jan-ƙafa wajen ɗaukar matakai inda yake aikata abu babu tsammani ko ma babu shawara; da ƙin yarda ya zama ɗan barandan Amurka, ko kuma a dinga mu'amalantarsa a matsayin shugaban wata wulaƙantacciyar ƙasa.
Jabri ya zargi MBS da satar sa-hannun sarki kan wani umarni da yake tura dakaru wajen aiki.
Jabri ya ce ya tattauna game da yaƙin Yemen a fadar White House kafin a fara shi; kuma Susan Rice, mai bai wa Shugaban Ƙasa Obama shawara kan tsaro, ta yi gargaɗin cewa hari ta sama kawai Amurka za ta goyi baya.
Amma Jabri ya yi iƙirarin cewa MBS ya kafe kan ra'ayinsa, inda ya yi watsi da Amurkawan.
"Mun yi mamakin ganin umarnin fada cewa dakaru su kutsa ta ƙasa," in ji Jabri. "Ya saci sa-hannun mahafinsa a kan wannan umarni saboda lafiyar sarkin ta fara taɓarɓarewa."
Jabri ya ce majiyarsa game da wannan zargi "sahihiya ce kuma abar dogaro" wadda ya alaƙanta da ma'aikatar harkokin cikin gida, wurin da ya yi aiki a matsayin shugaban ma'aikata.
Jabri ya ba da labarin yadda wani shugaban CIA ya nuna masa ɓacin rai kan MBS saboda ya ƙi bin shawarar Amurkan.
Tsohon shugaban MI6 Sir John Sawers ya ce bai sani ba ko MBS da gaske ya saci sa-hannun. "A bayyane take cewa ra'ayin MBS ne afka wa Yemen da dakarun soji, ba na mahaifinsa ba, duk da cewa shi ma ya amince a yi hakan."
Mun fahimce cewa MBS na kallon kansa a matsayin wani daban tun daga farkon lamari - matashi da ke da abubuwan da yake son nuna wa duniya da kuma ƙin bin umarninn kowa saɓanin nasa.
Kirsten Fontenrose, wadda ta yi aiki da tawagar tsaro ta tsohon Shugaban Amurka Donald Trump, ta ce lokacin da ta karanta nazarin hankalin da CIA ta yi a kan yariman, ta ji cewa ba su gane lamarin da kyau ba.
"Babu wasu misalai da za a iya gwada rayuwarsa da su," in ji ta. "Yana da abubuwa da yawa a hannunsa. Ba a taɓa hana shi wani abu ba. Shi ne matashin shugaba na farko da ya fara haska irin wannan ƙarni da ire-irenmu tsofaffi a gwamnati ba za su gane ba."
Tsara dokoki nasa na kansa
Cinikin wani shahararren zane da MBS ya yi 2017 na nuna irin yadda yake tunani, da kuma yadda yake da kasada, maras tsoron tunkarar martanin da al'ummarsa mai tsaurin ra'ayi za ta mayar. Sama da haka, ya mayar da hankali wajen nuna wa ƙasashe Yamma yadda ake shimfiɗa ƙarfin iko.
A 2017, rahotonni sun ambato wani yarima da MBS ya aika ya kashe dala miliyan 450 wajen sayen zanen hoton Salvator Mundi, wanda shi ne aikin ƙirƙira mafi tsada da aka taɓa sayarwa a duniya. An ce zanen ya shahara ne saboda Leonardo da Vinci ne ya yi shi, inda ya nuna Yesu. Yanzu shekara bakwai kenan da yin gwanjon zanen amma an neme shi an rasa.

Bernard Haykel, wani abokin yarima kuma farfesa a jami'ar Near Eastern Studies at Princeton University, ya ce duk da raɗe-raɗin cewa zanen yana rataye a jirgin ruwan MBS ko fadarsa, zanen yana ajiye a birnin Geneva kuma MBS na son rataye shi ne a wani wurin ajiyar kayan tarihi a birnin Riyadh na Saudiyya da ba a gina ba har yanzu.
"Ina son na gina babban wurin ajiyar kayan tarihi a Riyadh," kamar yadda Haykel ya ce MBS ya faɗa. "Kuma ina son wani babban abu da zai ja hankalin mutane kamar Mona Lisa."
Haka nan, manufarsa kan wasanni na nuna shi a matsayin mai cike da burika da kuma rashin tsoro.
Maƙudan kuɗin da Saudiyya ta kashe a fannin wasanni - kamar neman karɓar baƙuncin gasar Kofin Duniya ta 2034, da jarin da ta zuba a gasannin tennis da golf - wasu na kallon sa a matsayin "sportswashing" ko kuma "wanke laifi da wasanni". Amma abin da muka gani shi ne shugaban da bai damu da tunanin ƙasashen Yamma a kansa ba: tunaninsa shi ne zai iya yin komai wajen ganin ya inganta kansa da kuma Saudiyya.
"MBS ya fi damuwa da faɗaɗa mulkinsa a matsayinsa na shugaba," a cewar Sir John Sawers wanda ya taɓa haɗuwa da shi. "Kuma hanya ɗaya da zai iya yin hakan ita ce ya inganta ikon ƙasarsa. Shi ne abin da ke ba shi ƙarfin gwiwa."
Shekaru kusan 40 da jabri ya kwashe a matsayin jami'in gwamnatin Saudiyya sun gamu da cikas a yunƙurin kawo na MBS. Shugaban ma'aikatan tsohon yarima mai jiran gado Muhammad bin Nayef ya gudu daga ƙasar yayin da MBS ke shirin karɓar mulki, bayan wata hukumar leƙen asiiri ta ƙasar waje ta ankarar da shi cewa zai iya shiga cikin haɗari. Amma Jabri ya ce MBS ya aika masa saƙon tes kuma ya ba shi damar cigaba da aikinsa.
"Tarko ne - ni kuma ban faɗa ba," in ji Jabri, yana mai cewa za a iya azabtar da shi, ko kulle shi, ko ma a kashe shi idan ya koma. Haka kuwa aka yi yayin da aka kama 'ya'yansa Omar da Sarah kuma aka garƙame su saboa zargin halasta kuɗin haram da kuma yunƙurin guduwa, amma sun musanta zargin. Wani kwamatin yaƙi da tsare mutane na Majalisar Ɗinkin Duniya ya nemi a sake su.
"Ya tsara kashe ni," in ji Jabri. "Ba zai huta ba har sai ya ga bayana, ba ni da wata tantama a kan haka."
Hukumomin Saudiyya su sha neman a mayar da Jabri gida daga Canada amma hakan ya ci tura. Sun yi iƙirarin ana tuhumar sa ne da cin hancin biliyoyin dala lokacin da yake ma'aikatar harkokin cikin gida. Amma an ba shi muƙamin manjo janar kuma CIA da MI6 sun yabe shi game da daƙile hare-haren ƙungiyar al-Ƙa'ida.
Kisan Khashoggi
Kisan Jamal Khashoggi a ofishin jakadancin Sauidiyya da ke birnin Istanbul na Turkiyya a 2018 na nuna hannun MBS ta hanyoyi da dama da zai yi wuya ya iya musantawa.
Mutum 15 sun je da fasfo samfurin difilomasiyya kuma cikinsu akwai masu gadin MBS kansa. Daga baya an tsinci gawar Khashoggi da aka yi imanin cewa an gididdiba shi ne da ƙarafuna.
Fafesa Haykel ya yi hira da MBS ta WhatsApp jim kaɗan bayan kisan. "Na tambaye shi, 'Ta yaya haka za ta faru? Ina ganin shi ma ya girgiza. Bai san abin zai zama haka ba."
Dennis Ross ya haɗu da MBS bayan haka. "Ya ce ba shi ne ya aikata [kisan] ba kuma kuskure ne," in ji Ross. "Tabbas na so na yarda da shi, saboda ba na tunanin zai iya ba da umarnin aikata irin wannan abu."

MBS ya sah musanta hannu a shirin kisan, duk da cewa a 2019 ya "ɗauki alhaki" saboda laifin ya faru ne a ƙrƙashin ikonsa. Wani rahoton sirri na gwamnatin Amurka da bayyana a Fabrairun 2021 ya ce yana da hannu a kisan Khashoggi.
Na tambaye mutanen da suka san MBS kan ko ya koyi darasi; ko kuma kuɓutar da ya yi daga zargin kisan Khasoggi ta ƙara tsaurara tunaninsa.
"ya koyi darussan ta hanya mai wuya," a cewar Farfesa Haykel, wanda ya ce MBS ya tsani yadda ake yawan ɓata sunansa da na ƙasarsa game da kisan, amma kuma za a iya maimaita kisa irin na Khashoggi.
Sir John Sawers na ganin kisan wani sabon babi ne. "Ina ganin ya koyi darussa. Amma kuma shi bai sauya ba."
Mahaifinsa Sarki Salman ya kai shekara 88 yanzu. Idan ya rasu MBS zai iya mulkar Saudiyya tsawon shekara 50 masu zuwa.
Sai dai, a kwanan nan ya aminta cewa yana fargabar a kashe shi, musamman saboda yana yunƙurin kyautata alaƙar Saduiyya da Isra'ila.
"Ina ganin mutane da dama da ke son kashe hsi," a cewar Farfesa hakel, "kuma ya san hakan."
Ankarewa tsawon rayuwa ne ke sa mutane irinsu MBS su tsira da rayuwarsu. Shi ne abin da Saad al-Jabri ya lura da shi tun lokacin da MBS ya fara samun iko, lokacin da ya fizge wayar tarho daga jikin soket kafin ya fara magana a fadarsa.
Har yanzu MBS na cike da burin zamanantar da ƙasarsa ta hanyoyin da waɗanda ya gada ba za su taɓa iyawa ba. Amma kuma ba shi ne ɗan kama-karyar da ya fara rungumar tsarin rashin tausayi ba ta yadda babu wani na kusa da shi da zai iya hana shi aikata kuskure.