by MUHAMMAD AUWAL UMAR
July 22nd 2024.

Me ya haddasa saɓani tsakanin Dangote da hukumomi a Najeriya?

Aliko Dangote

ASALIN HOTON,YOUTUBE/MO IBRAHIM FAOUNDATION

  • Marubuci,Awwal Ahmad Janyau
  • Sanya sunan wanda ya rubuta labari,BBC Hausa, Abuja

Saɓani tsakanin Aliko Dangote, mutumin da yafi kowa arziki a Afrika da kamfanin man fetur na NNPC game da matatarsa na ci gaba da jan hankali a Najeriya.

Matatar mafi girma a Afirka wadda aka kashe dala biliyan 20 a wajen gina ta a Lagos, mallakin Aliko Dangote, attajirin da ya fi kowa dukiya a Afirka, an sa ran za ta kawo ƙarshen dogaron da Najeriya ke yi da man fetur da ake shigowa da shi daga waje har ma da tallafa wa maƙwaftan ƙasashe.

Amma tun bayan fara aiki a watan Janairu, matatar ta Dangote ta riƙa samun saɓani da kamfanin mai na Najeriya NNPCL, inda kamfanin ya fara cewa sinadarin sulfur da ke cikin man matatar ya zarta adadin da ake buƙata.

Saɓanin har ya yi zafin da har Aliko Dangote ya bayyana cewa a shirye yake ya sayar wa NNPCL da matatar ta biliyoyin daloli.

"NNPCL na iya sayen matatar don tafiyar da ita yadda yake so. Sun bayyana ni a matsayin mai babakere a harkar kasuwanci. Wannan ba gaskiya ba ne kuma bai dace ba, amma babu laifi. Idan za su saya, aƙalla za su yi maganin wanda suka kira mai babakere," kamar yadda Dangote ya shaida wa jaridar Premium Times.

Abubuwan da suka faru

  • Akwai yarjejeniya tsakanin matatar Dangote da kamfanin NNPC tun kafin soma aikin matatar, amma matatar Dangote ta ce kashi bakwai kawai kamfanin ya biya na hannun jari kafin cikar wa'adin yarjejeniyar maimakon kashi 20.
  • Matatar man Dangote ta ce tana fatan samar da gangar mai 550,000 a bana, amma kuma kamfanin Dangote ya ce dole sai ya nemi wasu hanyoyin samun ɗanyen mai daga ƙasashen waje saboda rashin wadatarsa a cikin gida.
  • Matatar ta ce jirgin ruwa biyar na ɗanyen man fetur kawai ta samu tun fara aikinta daga kamfanin NNPCL, maimakon 15 da ta yi tsammani.
  • Matatar Dangote kuma ta yi zargin cewa ana shigo da gurɓataccen mai a Najeriya.

Wannan ne ya sa kamfanin mai na ƙasar ya mayar da martani kan dalilin ƙaurace wa bai wa matatar isasshen ɗanyen mai:

  • NNPCL ya ce sinadarin sulfur ya yi yawa a ɓangaren man dizel da matatar Ɗangote ke samarwa.
  • A makon da ya gabata shugaban hukumar kula harkar man fetur ta Najeriya (NMDPRA) Farouk Ahmed, ya faɗa wa taron manema labarai cewa "man fetur ɗin matatar Dangote bai kai ingancin wanda ake shigowa da shi ba".

Sai dai a martaninta, matatar Dangote ta ce an samu matsalar sinadarin sulfur mai yawa ne lokacin da ta fara aiki a farkon shekarar nan, amma yanzu an rage sinadarin da kuma zai ci gaba da raguwa yayin da aiki ke ci gaba da tafiya.

Matatar ta ce yanzu ta daidaita sinadarin na sulfur da ke inganta mai daga wari ko nauyi, kamar yadda kamfanin Dangote ya bayyana cikin wata sanarwa bayan ziyarar da kwamitin harakokin man fetur na Majalisar wakilan tarayya ya kai a matatar a ƙarshen mako.

Matatar Dangote ta kuma ce tana tattaunawa da ƙasashen Libya da Angola domin samo ɗanyen mai bayan rashin samun wadatarsa a Najeriya, ƙasar da ta fi arziƙin mai a Afirka.

Me saɓanin ke nufi?

Matatar Dangote

ASALIN HOTON,OTHER

Masana tattalin arziki da na albarkatun man fetur na ci gaba da sharhi kan saɓanin da ya kunno kai tsakanin kamfanin mai na NNPCL da matatar Dangote.

Hada-hadar mai, babbar kasuwa ce a duniya. Dr Isiyaku Shi'itu Almustapha, malami a Jami'ar Canterbury Christ Church da ke Birtaniya na ganin saɓani tsakanin hukumomi a Najeriya da matatar Dangote babban ƙalubale ne ga tattalin arziƙin Najeriya.

Ya ce saɓanin na nufin akwai matsala ga yarjejeniyar da ɓangarorin biyu suka ƙulla.

Masana albarkatun man fetur irin su Farfesa Ahmed Adamu na ganin saɓani tsakanin gwamnati da Dangote wani ci baya ne ga fatan da ƴan Najeriya ke da shi na cin moriyar tasirin matatar man Dangote idan har ta soma aiki gadan-gadan.

Masanin ya danganta saɓanin da siyasa da kuma hamayyar kasuwanci.

Farfesa Ahmed ya ce duk da zai yi wahala a ce Najeriya ta yi dogaro kacokan da matatar Dangote, amma kwatanta shi da 'mai yin babakere' a harkar kasuwanci kamar karya masa gwiwa ne - "domin shi kaɗai ne ya ji zai iya asassa matatar man fetur a ƙasar duk da na gwamnati ba su aiki," in ji shi.

Masanin yana ganin kasancewar matatar ƴar Najeriya kuma ta ɗan Najeriya ya kamata idan har akwai matsala gwamnati ta magance ta ba tare da an ji tsakaninsu da kamfanin Dangote ba.

"A ce ga naka a gida amma ka tsallake ka je ka saye na wani, hakan ya nuna ba ka bai wa naka goyon bayan da ya kamata ba - kamar wannan ya nuna gwamnati ba ta da ra'ayi da matatar."

"Wannan alamu ne da ke nuna ba za a samu tasiri ko ci gaban da ake fatan samu ba albarkacin matatar Dangote," a cewar Farfesa Ahmed.

Ya ƙara da cewa saɓanin ya nuna kamar ana tursasa wa kamfanin yin hamayyar kasuwanci ne da na ƙasashen waje.

Nau'in ɗanyen mai na Najeriya yana cikin waɗanda ake so a duniya saboda rashin warinsa da nauyi. Kuma masana na ganin rashin samun na Najeriya na iya sa ya samu tangarɗa wajen samar da wanda gwamnati ke ɓukata.

Amma a cewar Farfesa Ahmed, yanzu Najeriya abin da take buƙata shi ne man fetur mai arha da kuma yadda tattalin azikin ƙasar zai farfaɗo. "Sai an cimma wannan sannan ya kamata a fara maganar inganci" in ji shi.

rashin samun na Najeriya na iya sa ya samu tangarɗa wajen samar da wanda gwamnati ke ɓukata.

Amma a cewar Farfesa Ahmed, yanzu Najeriya abin da take buƙata shi ne man fetur mai arha da kuma yadda tattalin azikin ƙasar zai farfaɗo. "Sai an cimma wannan sannan ya kamata a fara maganar inganci" in ji shi.

Me ya kamata a yi?

Masana na ganin ya kamata a sasanta a fahimci juna.

Farfesa Ahmed ya ce ya kamata gwamnati ta yarda cewa matatar Dangote ba ta Aliko Dangote ba ce - duk da kashe kudinsa da ya yi amma ci gaban tattalin arzikin Najeriya ne.

A cewarsa, "duk wanda ya nemi ya durkusar da matatar Dangote yana neman ya durkusar da tattalin arzikin Najeriya ne."

"Sannan saɓa wa ƴan kasuwa irin su Dangote zai karya gwiwar masu saka jari saboda yana iya fusata shi ya daina zuba jarinsa a Najeriya ya ƙetara zuwa wasu ƙasashen," in ji shi.

Masanin ya ƙara da cewa ya kamata gwamnati ta zauna da Dangote a fahimci juna tare da ba shi duk goyon bayan da yake bukata.

"Abin da ya kamata, NNPCL ta fara tayin sayen mai daga matatar Dangote kafin fita waje"

Idan aka bai wa Dangote kwarin gwiwar da yake bukata har matatar ta samu haɓaka da bunƙasa - wani ƙwarin gwiwa ne ga masu zuba jari su shigo Najeriya," a cewar Farfesa Ahmed.

Dr Isiyaku Shi'itu Almustapha malami a Jami'ar Canterbury Christ Church a Birtaniya na ganin matsalar ta kai girman da ya kamata shugaban kasa ya zauna da Aliko Dangote a sasanta ko a samu shiga tsakanin tsoffin shugabannin ƙasa.

Matatar Dangote ta kasance wani kasuwanci mafi girma na kamfani mai zaman kansa da ya zuba hannu jari a Najeriya.

Bayanai sun ce matatar na shirin faɗaɗa man da take fitarwa zuwa wasu ƙasashen yammacin Afirka, inda matatar za ta iya mamaye kasuwancin mai a yankin.

Sai dai ana ganin wannan saɓanin tsakanin gwamnatin Najeriya da kamfanin har ya kai ana ruwaito Aliko Dangote na cewa 'ya fara yin nadama'.

MUKHZAFAYA GLOBAL RAHAMANIYA ENTERPRISES user

MUHAMMAD AUWAL UMAR

[email protected]
Search Website

Search

Subscribe

Newsletter

WhatsApp Google Map

Safety and Abuse Reporting

Thanks for being awesome!

We appreciate you contacting us. Our support will get back in touch with you soon!

Have a great day!

Are you sure you want to report abuse against this website?

Please note that your query will be processed only if we find it relevant. Rest all requests will be ignored. If you need help with the website, please login to your dashboard and connect to support