*AHLIL-KISA'I DARUL-MUIQAMATY*
*ZUBAR DA JINI DA KARKASHE "YA'YAYEN ANNABI(S) DA WASU SUKA YI, A CIKIN ADDININ NAN😭*
*~(KASHI NA 16)~*
*YA UBANGIJI, MAFI GIRMAN SALATY DA AMINCI DA GAISUWARKA SUYI TA GUDANA GA KYAKKYAWAN BALARABANKA S.A.W. TARE DA IYALANSA TSARKAKAN MA'ASUMAI, DA KUMA DUK SAHABIN DA YAKE DA GIRMA A ZUCIYAR SAYYIDA FADIMA A.S*
*⚡:اَلسَلامُ عَلَی الْحُسَیْنِ وَعَلی عَلِیِّبْنِ الْحُسَیْنِ وَعَلی اَوْلادِ الْحُسَیْنِ وَعَلی اَصْحابِ الْحُسَیْنِ علیہ اسلام🚩🙌*
*Bayan ibnu ziyad L.A yace a saka Su Sayyida Zainab a Kurkuku a Garqamesu, sai ya rubutawa yazidu dan mu'awiya wasika cewa Ya kashe Imam Hussain A.S, da dukkan sahabban sa, kuma ya kamo mata da 'Ya'yan sa, sai Yazidu L.A ya bashi umarni cewa a kawo masa kawuka da kamammun da aka kama, Hedikwatar mulkinsa ta sham wato (Dimashqa).*
*Ibnu ziyad L.A ya umarci dakarunsa cewa, Ariqa bi gari-gari ana nuna su, kuma kowanne gari a kaje, a umarci mutanen garin su fito su rinqa tofa nusu yawu da kaki, kuma su rinqa watsa musu kasa da yi musu Isgilanci!*
*Wannan ne yasa Tafiyar da akayi da su sayyada Zainab tayi tsaho sosai, domin ba mikakkiyar Tafiya akayi ba, an yi ta zagayawa dasu ne garuruwa don a nuna su kuma a wulakanta su!*
*An share kwanaki ana Tafiya, Sayyida Zainab ta galabaita kwarai! Domin ita ke kula da dukkan mata da yaran da aka kamo, ko jinyar Raunukan mata, ko kula da marar lapiya Zainal-Abidin, ko Rarrashin marayun da suka rasa Iyayen su.*
*Bata samu damar bacci ba, sai bayan tsahon kwanaki! Ana Tafiya ne dare yayi sosai, sai aka yada zango za'a kwana, bayan sayyida Zainab ta yi hidimar da ta saba, mata da yara sunyi bacci, tana zaune sai bacci ya sace ta saboda Gajiya!*
*Marubucin littafin "MA'ALIYAL SIBDAIN" Ya ce:*
*~Sai Sukaina "Yar Imam Hussain A.S ta farka ta fashe da kuka, saboda ta tuna lokacin da mahaifinta ke raye da irin mutuntawa da karramawar da yake yi mata, da kuma cewa yanzu ga ta a Qaskance cikin wulakanci! Sai ta yi ta rusa kuka!.*
*Wani daga fadawan yazidu yazo ya same ta ya ce mata: "ki yi mana shiru! Kin dame mu da kukan nan naki, Sukaina ba ta kula da shi ba saboda tsanantar kukanta,Ta yi ta rusa kuka tana sheshsheqa kamar zata mutu!*
*Sai bafaden nan ya ce: ke 'Yar gidan dan tawaye! Ki yi mana shiru! Sukaina najin wannan kalma sai ta kwalla ihu ta ce: Wayyo Babana! Babana sun kashe ka bisa zalunci! Kuma gashi suna ce maka dan tawaye!! Sai bafaden nen ya harzuka, ya fincikota ya jata a kasa ya kaita daji ya wurgar da ita! Tana faduwa sai ta suma nan take! Ba ta farfado ba sai kusan Asuba, a lokacin kuma tawaga ta kama hanya ta tafi!*
*Duk wannan abin da ya faru sayyida Zainab bata sani ba! Saboda nauyin bacci na gajiya, kuma da yake dare ne har aka kama hanya ba ta lura cewa Sukaina ba ta nan ba.*
*Ita kuma Sukaina da ta farfado sai ta rasa inda take, ta tashi tana tafiya bata sam inda zata ba! Ta fadi ta tashi! Zuwa can sai ta tsuguna Ta Roki Allah, ta nemi Taimakon Babanta da kakanta Manzon Allah(S),*
*Tayi ta yawo a daji ba ta ga ko alamar tawagar su Sayyida Zainab ba, sai kawai ta yanke jiki ta fadi a sume! A daidai lokacin da Sukaina ta fadi ta suma, sai kawai Mashin da aka tsire Kan Imam Hussain a jiki ya Qwace daga hannun mai Rikon sa ya fado, Qasa ta tsage Rabin Mashin ya nutse a cikinta ta Rike shi!*
*Mu hadu a kashi na 17 da Yardar Allah*
*:🚩🚩:اسلام عليک يا ابا عبدالله الحسين علیہ سلام🙏*
*Zamzam Baqurasshen Umma