Yadda wata mata ta ƙona kanta a Jigawa

Mata a cikin damuwa

ASALIN HOTON,GETTY IMAGES

Al'ummar ƙauyen Garin Mallam da ke yankin ƙaramar hukumar Guri na cikin alhinin da ya girgiza zukatansu bayan da wata mata mai shekara 40, ta cinna wa kanta wuta, bayan ta yayyafa wa kanta fetur a wani daji da ke wajen ƙauyen.

Rundunar ƴansandan jihar ta tabbatar da aukuwar lamarin, inda ta ce tana gudanar da bincike domin gano haƙiƙanin abin da ya yi sanadiyyar lamarin.

Sai dai ’yansandan sun ce binciken farko-farko da suka gudanar ya nuna cewar marigayiyar ta hallaka kanta ne saboda tsananin damuwa da take ciki bayan mutuwar aurenta a watannin da suka gabata.

Bayanai sun ce matar mai suna Fatsuma Bagobiri ta tafi cikin daji ne, domin guje wa mutane inda daga nan ne ta aikata abin da ta aikata.

'Tana fama da matsalar damuwa'

Kakakin rundunar 'yansandan jihar Jigawa, DSP Lawan Shiisu Adam ya shaida wa BBC cewa binciken farko da 'yansanda suka gudanar ya nuna cewa tana fama da matsananciyar damuwa sakamakon sakin ta da mijinta ya yi a watannin da suka gabata.

''Da tana da aure, sai kuma daga baya suka rabu da mijinta, wannan abu kamar shi ne ya tunzura ta har ta samu damuwa matsananciya, har ta aikata wannan al'amari,'' in ji shi.

Ya ƙara da cewa a baya an yi zargin cewa matar ta taɓa yunƙurin ƙona kanta, amma ba ta yi nasara ba.

Jami'in 'yansandan ya kuma ce akwai wasu bayanai da ke nuna cewa dama mutanen gidan marigayiyar suna da cutar ta damuwa.

''Muna da bayanin cewa dama 'yan gidansu na da wannan cuta ta damuwa'', in ji shi.

Amma DSP Shiisu ya ce bayanan da suke samu shi ne matar ta kamu da damuwar ne sakamakon rabuwarta da mijinta.

Ya kuma ce rundunar 'yansanda za ta gayyaci tsohon mijin nata da sauran 'yan'uwanta domin samun ƙarin bayanai.

Mutuwar aure dai wani lamari ne da ya zamo tamkar ruwan dare a wasu jihohi na arewacin Najeriya.

Kuma a mafi yawan lokuta lamarin ya fi zamewa mai wahala ga matan da abin ya shafa, kasancewar matan aure da dama sun dogara ne kacokan kan mazajensu wajen samun abinci da sauran bukatu na rayuwa.

Saboda haka barin gidan miji na nufin irin wadannan mata kan rasa irin wannan tallafi, wanda hakan a lokuta da dama kan jefa su cikin kunci musamman idan ba su samu kwanciyar hankali a tsakanin iyalansu da za su koma cikinsu ba.

'Gawar ta ƙone sosai'

DSP Lawan Shiisu ya ce jami'an 'yansanda sun tsinci gawarta a dajin, bayan da ta gama ƙonewa.

''Ta yi amfani da man fetur da ta saya, ta kwarara wa kanta sannan ta ƙyasta ashana in da ta banka wa kanta wuta, ta kuma ƙone gaba ɗaya,'' in ji shi.

Labarin mutum ya kashe kansa sakamakon wata damuwa da yake fama da ita, ba sabon abu ba ne, to sai dai irin wannan salon na ƙona kai, abu ne da ba a taɓa jin irinsa ba a baya-bayan nan.

Me ke janyo cutar tsananin damuwa?

Dakta Dayyaba Shaibu, ƙwararriyar likitar lafiyar ƙwaƙwalwa a Abuja, ta ce cutar tsananin damuwa na iya kama kowane jinsi na mutane, sannan ana ganinta a manya da yara duka.

Sai dai ta ce an fi ganin ta a mata da matasa da suke daidai shekarun balaga.

Masana lafiyar ƙwaƙwalwa sun ce sau da yawa idan wani iftila'i ya samu mutum ne yake shiga halin tsananin damuwa, kamar rasa wani makusanci, ko kora daga wajen aiki, ko haihuwa mai cike da tangarɗa, da dai sauransu.

Dakta Ɗayyibah ta ce yanayin halittar ɗan'adam na taka muhimmiyar rawa wajen samun wannan matsala.

"Wani Allah ya halicce shi da juriya. Ko da abin tashin hankali ya same shi zai daure kuma ba zai zauna masa a rai ba.

"Wani kuma ba shi da haka. Allah ya halicce shi yana da rauni kuma ba shi iya jure jarrabawa. To irinsu ne suka fi gamuwa da matsalar tsananin damuwa," a cewar likitar.

Amma ta ce wani lokaci ma haka kawai mutum kan shiga damuwa har ta zamar masa wannan cuta.