by MUHAMMAD AUWAL UMAR
August 4th 2024.

*AHLIL-KISA'I DARUL-MUQAMATY*

*UMMUL-MASA'IB WATO MACEN DA TAFI KOWACCE MACE GANIN MUSIBA A RAYUWA.. ZAINAB A.S😭*


            ~*KASHI NA (5)*~
*TAFIYE-TAFIYEN DA SAYYIDA ZAINAB TAYI A RAYUWA😭*

*اَلسَلامُ عَلَی الْحُسَیْنِ وَعَلی عَلِیِّبْنِ الْحُسَیْنِ وَعَلی اَوْلادِ الْحُسَیْنِ وَعَلی اَصْحابِ الْحُسَیْنِ علیہ اسلام*

*Nana Zainab ta kasance cikin Jarrabawowi da Manyan Masifu, domin ta shaidi masifar da ta auku a yaqin Jamal, inda Rayuwkan sahabban Annabi(S) sama da dubu 16 suka salwanta, da Yaqin Siffin, inda Rayuka sama Dubu 33 suka salwanta, da Nahrawan inda sama da Rayuka Dubu 7 suka salwanta.*

*Kwatsam sai kuma ga shi ta tsinci kanta A Filin Karbala! Inda aka yiwa Musulimci Mummunan Ta'adin da ba'a tab'a irinsa ba, kai a Duniya ma ba'a tab'a irin wannan Bala'in ba! aka nemi karar da zuri'ar Annabi(S) da share ta daga doran kasa bakidaya!*

*Sayyida Zainab S.A ta na cikin Iyalan Annabi(S) da aka tsare a karbala, aka killace su daga Abinci da Ruwan sha tsahon kwana 3, Yara Kanana jikokin Ahmadu(S) da ke killace ita suke zuwa su samu suna mata kuka cewa ta basu ruwa su sha, don tsananin Qishin Ruwa ya kama su!*

*Tana ji tana gani aka kashe 'Ya'yanta da 'Ya'yan wanta Imam Hassan A.S, da 'Ya'yan dan'uwanta Imam Hussain A.S, da sahabbansa da Shi kansa Imama Hussaini A.S, tana jin sautinsa tare da kallonsa a tsaye shi kadai a cikin Sahara, lokacin da ya ke cewa:*

*~"Shin ba wani mai taimako da zai Taimakemu? Shin ba wani mai kawo Gudun-mawa ga Mutuncin Manzon Allah(S)! Shiru kakeji Babu!😭*

*Lallai sayyida Zainab S.A ta ga Bala'o'i da masifu a Rayuwarta, Lallai ta cancanci Sunan "Alqiblar Bakin ciki!" Kuma ta dace da laqabin "Ummul-Masa'ib" Uwar Masifu!!*

*Allamah Al-Barghany cikin Littafinsa "Majlisul-Muttaqin" Ya fadi cewa: Matsayi na Musamman da Sayyida Zainab S.A ta taka a Irfani ya kusa kaiwa ga Matsayin Imamanci! Woto kujerar Manzon Allah(S) wacce ya Shugabantar a bayansa.*

*Marubucin littafin "Darrazil Mazhab" Ya ce: Girman Sha'anain Sayyida Zainab na Al'amuran Badini, da matsayinta na Ma'anawy Yafi yadda ake Fadi! Domin Falalarta da Fifikonta da Abubuwan da ta Kebanta da su, da Girman Matsayinta, da Zurfin Ilminta, da kyawawan Ayyukanta, da Ismah (Katanguwa daga sab'on Allah).*

*Da kuma Kamewarta, da Haskenta da kwarjininta, da Daukakarta, da Tasirinta, Duk ta ga ji Mahaifiyarta Sayyida Fadima Azzahrah S.A ne! Itace Khalifar Nana Fadima a duk wadannan Abubuwa da muka Ambata.*

*Marubucin littafin "Jannatil Khulud" Ya fadi bisa ma'ana cewa: Sayyida Zainab a fagen balagar magana, da gudun Duniya, da Iya Tafiyar da Al'amura, da Jarumta, sai dai a kwatantata da Mahaifinta Imam Aliy A.S Zakin Allah.*

*Da Kuma Mahaifiyarta Sayyida Fadima Azzahra S.A, domin Tafiyar da Al'amuran Ahlil baity A.S, da ma na dukkan Banu-Hashim bayan Shahadar Imam Hussain A.S na tafiya ne bisa Ra'ayi da Umarnin Sayyida Zainab A.S*

*Imamun Naisabury cikin littafin "Risalatul Alawiyyah" Ya ce: Sayyida Zainab 'Yar Imam Ali A.S a fagen fasaharta da Balagarta, da Gudun Duniyarta, da Ibadarta, Kamar Mahaifinta Murtadha da Mahaifiyarta Azzahrah A.S take!"*

*Mu hadu a kashi na 6 da Yardar Allah*

*Assalamu Alaiki Farin-Cikin Sayyida Zahra, Jindadin Sayyida Zahra, Ya wacce Take samar da Annushuwa da Sururi ga Sayyida Fadima, dama dukkan Dangin Banu-Hashim Bakidaya..*

*Zamzam Baqurasshen Umma na supy08033567648*

MUKHZAFAYA GLOBAL RAHAMANIYA ENTERPRISES user

MUHAMMAD AUWAL UMAR

[email protected]
WhatsApp Google Map

Safety and Abuse Reporting

Thanks for being awesome!

We appreciate you contacting us. Our support will get back in touch with you soon!

Have a great day!

Are you sure you want to report abuse against this website?

Please note that your query will be processed only if we find it relevant. Rest all requests will be ignored. If you need help with the website, please login to your dashboard and connect to support