by MUHAMMAD AUWAL UMAR
August 22nd 2024.

Labaran Duniya l BBC HAUSA 




Create Your Smart Website For Free


An yi wa Sarkin Gobir sallar janaza (Salatul Gha'ib)


Lokacin da ake yi wa Sarkin Gobir na Gatawa Isa Bawa sallar janaza a garin Sabon Birni na jihar Sokoto

ASALIN HOTON,FB/MUHD KABEER HARUNA

Bayanan hoto,Lokacin da ake yi wa Sarkin Gobir na Gatawa Isa Bawa sallar janaza a garin Sabon Birni na jihar Sokoto

Al'ummar garin Sabon Birni a jihar Sokoto sun gudanar da sallar janazar Sarkin Gobir na Gatawa, Isa Bawa da safiyar yau Alhamis, bayan kashe shi da ƴan bindiga suka yi.

Labarin kisan sarkin ya ɓulla ne a ranar Laraba, bayan da bayanai suka tabbatar da cewa ƴan bindigar sun halaka shi duk da neman kuɗin fansa da suka yi.

Ɗaruruwan mutane ne suka hallara domin gudanar da sallar a garin Sabon Birni.

...

ASALIN HOTON,FB/MUHD KABEER HARUNA

Kisan basaraken na zuwa ne bayan ya shafe sama da mako uku a hannun ƴan bindigar waɗanda suka ɗauke shi a kan hanyarsa ta zuwa wani taro.

Tuni shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya miƙa ta'aziyya ga iyalai da kuma masarautar ta Gobir, tare da yin alƙawarin kawo ƙarshen matsalar tsaro a yankin.

...

ASALIN HOTON,FB/MUHD KABEER HARUNA

Sokoto na daga cikin jihohin arewa maso yammacin Najeriya da ke fama da matsalar ƴan fashin daji masu kisa da kuma garkuwa da mutane domin neman kuɗin fansa.

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta sha iƙirarain cewa tana bakin ƙoƙarinta wajen magance matsalar, sai dai har yanzu abin bai yi sauƙi ba a wasu sassan ƙasar.

Jihohin Katsina, Zamfara, Sokoto, Neja da Kaduna na cikin jihohin da matsalar ta fi yin ƙamari.

MUKHZAFAYA GLOBAL RAHAMANIYA ENTERPRISES user

MUHAMMAD AUWAL UMAR

[email protected]
Search Website

Search

Explore

Categories

Subscribe

Newsletter

WhatsApp Google Map

Safety and Abuse Reporting

Thanks for being awesome!

We appreciate you contacting us. Our support will get back in touch with you soon!

Have a great day!

Are you sure you want to report abuse against this website?

Please note that your query will be processed only if we find it relevant. Rest all requests will be ignored. If you need help with the website, please login to your dashboard and connect to support