by MUHAMMAD AUWAL UMAR
July 30th 2024.

BBC HAUSA Labarai Masu kutse a Koriya ta Arewa na ƙoƙarin sace bayanan sirri kan haɗa makaman nukiliya

..

ASALIN HOTON,OTHERS

Masu kutse a Koriya ta arewa na ƙoƙarin sace bayanan haɗa makamin nukiliya da bayanan sirrin sojoji daga kamfanoni da kuma ma'aikatun gwamnati a faɗin duniya, kamar yadda Birtaniya da Amurka da Koriya ta Kudu suka yi gargaɗi.

Sun ce ƙungiyar masu kutsen mai suna Andariel da Onyx Sleet - na kai hari kan kamfanonin tsaro da na sararin samaniya da nukiliya domin samun muhimman bayanai da nufin inganta ayyukan sojojin Pyongyang da shirye-shiryenta na nukiliya.

Ƙungiyar na neman bayanai daga ɓangarori da dama kuma tana neman bayanan ne daga Birtaniya da Amurka da Koriya ta Kudu da Japan da Indiya da wasu wuraren.

Bayanai sun ce masu kutsen na ƙoƙarin samun bayanai daga sansanin sojojin saman Amurka da hukumar sararin samaniyar Amurka Nasa da kamfanonin tsaro.

Wannan gargaɗi dai alama ce cewa ayyukan ƙungiyar na leƙen asiri da samun kuɗi abin damuwa ne ga jami'ai saboda tasirin hakan ga fasaha da kuma rayuwar yau da kullum.

Amurka ta ce ƙungiyar na tallafa wa masu yi mata leƙen asiri da kuɗaɗen da suke samu daga sace bayanan cibiyoyin kula da lafiya na Amurka.

MUKHZAFAYA GLOBAL RAHAMANIYA ENTERPRISES user

MUHAMMAD AUWAL UMAR

[email protected]
Search Website

Search

Subscribe

Newsletter

WhatsApp Google Map

Safety and Abuse Reporting

Thanks for being awesome!

We appreciate you contacting us. Our support will get back in touch with you soon!

Have a great day!

Are you sure you want to report abuse against this website?

Please note that your query will be processed only if we find it relevant. Rest all requests will be ignored. If you need help with the website, please login to your dashboard and connect to support