"BBC News, Hausa
Dole a faɗa wa shugaban ƙasa gaskiya - Ndume
ASALIN HOTON,OTHER
Ɗan majalisar dattijan Najeriya mai wakiltar Borno ta arewa, Sanata Ali Ndume - wanda aka sauke daga muƙamin mai tsawatarwa na majalisar - ya ce bai yi nadama kan kalamansa da suka kai ga tsige shi daga muƙamin nasa ba.
Sanatan ya bayyana haka a tattaunawar da ya yi da ƴan jarida, karon farko bayan matakin da majalisar ta ɗauka kan shi a ranar Laraba.
Sanatan ya ce abin da ya sa bai yi gaugawar mayar da martani ba saboda yana jimamin rasuwar da aka yi masa a jiharsa ta Borno
Ya ce bayan abin da ya faru, ya zauna ya sake yin nazari kan kalamansa, "kuma ban ga wani aibi ba kan abin da na faɗa."
"Na nemi taimakon shugabannin ƙasar nan da aminai su sake nazari kan kalaman su faɗa min ko abin da na faɗa ba haka ba ne ko na yi kuskure - amma dukkaninsu sun ce ba su ga wani aibi ba kan abin da na fada," in ji Sanata Ndume.
A ranar Laraba ne, Majalisar dattawan Najeriya ta tsige sanata Ali Ndume mai wakiltar Borno ta Kudu, daga muƙamin mai tsawatarwa bayan caccakar gwamnatin Bola Ahmed Tinubu.
Majalisar ta ce ta ɗauki matakin ne bayan ƙorafin jam'iyyar APC, mai mulki ta yi kan kalaman na Ndume.
Kuma nan-take majalisar ta zaɓi Sanata Tahir Munguno domin maye gurbin Sanata Ali Ndume.
Martanin Sanata Ali Ndume
A wani taron manema labarai da ya gudanar a jiharsa ta Borno a ranar Juma'a ya ce kalamansa ba su yi girman da za su kai ga ɗaukar matakin tsige shi ba.
"Ni ina ganin babu abin da na faɗa wanda ba daidai ba - don haka ina nan kan kalamaina a hirar da na yi," in ji shi.
Sanatan ya yi watsi da tayin da aka yi masa na shugaban kwamitin harkokin yawon shaƙatawa, yana mai cewa ba shi da wata ƙwarewa kan sha'anin yawon buɗe ido.
Game da jam'iyyarsa ta APC wadda ta buƙaci a tsige shi, Sanata Ndume ya ce "na ɗauki wannan a matsayin ƙaddara, domin Allah ne ya ba ni wannan muƙamin."
"Ba takara na yi ba aka naɗa ni matsayin mai tsawatarwa, ba takara na yi aka ba ni mataimakin shugaban kwamitin kasafin kuɗi ba, illa takarar sanata na yi a majalisar tarayya, kuma Allah ya ba ni, don haka Alhamdulillah".
Sanata Ndume ya kuma ari kalaman tsohon shugaban Amurka inda ya ce "zan yi amfani da kalaman tsohon shugaban Amurka Franklin D Roosevelt yana cewa:
"Ba kishin ƙasa ba ne, ka goyi bayan shugaban ƙasa kan dukkanin abin da ya yi - kishin ƙasa shi ne fadin gaskiya ba wai ga shugaban ƙasa kawai ba amma ga kowa."
"Ba kishin ƙasa ba ne ka ɓoye gaskiya ga masu mulki, kai har ga kowa ma. Dole a faɗa wa shugaban ƙasa gaskiya kuma na yi imani da waɗannan kalaman. kuma Allah yana tare da mai gaskiya, "
"Don haka na sani ban yi kuskure ba, mutane ba su yi kuskure ba saboda faɗin gaskiya da kuma tsayawa kan gaskiya."
"Don haka ina ƙara jaddada wa shugaban ƙasa ya koma ya sake nazarin kan kalaman da na yi domin ɗaukar matakan da suka dace wajen samar wa ƴan ƙasa sauƙi kan halin da suke ciki."
Ko Ndume zai fice daga APC?
Sanatan ya yi magana kan makomarsa a jam'iyyarsa ta APC da ta ce ya saɓa mata.
Ya ce yana cikin waɗanda suka assasa jam'iyyar APC. "Zan iya cewa na ma riga shugaban APC (Ganduje) shiga APC," in ji Ndume.
Ya ƙara da cewa yana cikin sanatoci 22 daga PDP suka kafa APC, lokacin da shugaban jam'iyyar na yanzu Abdullahi Umar Ganduje yana mataimakin gwamna.
ASALIN HOTON,SENATENG
Ali Ndume, sanata ne wanda ya yi suna wajen sukar manufofin gwamnati, yayin da magoya bayansa ke masa kallon mai faɗin albarkacin bakinsa ba tare da tsoro ba.
Wannan dai ba shi ne karo na farko da Majalisar Dattijan Najeriyar ta dakatar da wani wakili na ta ba.
Ko a watan Maris ɗin 2024 majalisar ta dakatar da Sanata Abdul Ningi mai wakiltar mazaɓar Bauchi ta tsakiya daga majalisar bayan zargin sa da furta "kalamai da ke iya zubar da ƙimar majalisar."
Majalisar ta ɗauki matakin ne bayan wata tattaunawa da sanatan ya yi da kafar yada labarai ta BBC, inda ya yi zargin cushe a cikin kasafin kudin ƙasar.