Fyaɗe da kisan likita ya janyo zanga-zanga a asibiti a India

Cikin dare ranar Juma'a wata likita mai neman kwarewa mai shekara 31, ta je ta kwanta a dakin taro na daya daga cikin asibitoci mafiya dadewa a Indiya bayan sun sha aiki.
Kuma wannan ne lokaci na karshe da aka gan ta a raye.
Gari na wayewa sai abokan aikinta suka ga gawarta a kan dandamalin gabatar da jawabi na zauren, rabi tsirara, ga kuma raunuka an ji mata.
Daga bisani 'yansanda sun kama wani mai aikin sa-kai a asibitin na koyarwa na Kwalejin RG Kar Medical mai shekara 138.
Dubban mata ne a Kolkata da kuma fadin jihar West Bengal ake sa ran za su yi wani gangami na neman 'yancinsu na rayuwa ba tare da tsoro ko fargaba ba a ranar Laraba.
Za a yi ganagamin ne kwana daya kafin ranar bikin samun 'yancin kasar ta India - wato ranar Alhamis.
Likitoci da suka harzuka sun dakatar da aiki a birnin da kuma fadin kasar ta India suna neman gwamnatin tarayya ta yi wata doka mai tsanani da za ta kare su.
Lamarin kisan likitar ya kara fitowa fili da irin cin akubar da likitoci da ma'aikatan jinya ke sha a kasar.
Ana samun rahotanni da dama na muzguna wa likitoci maza da mata -inda marassa lafiya ko danginsu ke ci wa likitoci mutunci.
Mata wadanda sun kai kashi 30 cikin dari na likitocin Indiya kuma kashi 80 cikin dari na ma'aikatan jinya a kasar sun fi takwarorinsu maza fuskantar hadarin muzgunawar
Fyade da kisan da aka yi a wannan asibiti na Kolkata ya kara fitowa da fili irin mummunan hadarin da ma'aikatan lafiya ke fuskanta a asibitocin asibitocin India.

A wannan asibiti na Kolkata ( RG Kar Hospital) , wanda ake kula da marassa lafiya 3,500 a kullum, likitoci masu neman kwarewa, da ke shan aiki fiye da kima inda wani lokaci suke aiki tsawon sa'a 36 ba hutu - babu wasu dakuna da aka ware na musamman na hutawarsu, wanda hakan ya sa dole suke zuwa dakin taro na asibitin da ke hawa na uku.
Rahotanni sun ce na'urar daukar hoto ta tsaro (CCTV) ce ta nuna, ma'aikacin sa-kan wanda aka kama bisa zargin laifin, wanda kuma daman ya yi kaurin suna a asibitin.
'Yansanda sun yi zargin cewa ba a gudanar da kyakkyawan bincike a kan mutumin ba kafin a dauke shi aiki.
"Asibitin shi ne kusan gidanmu na farko ; muna zuwa gida ne kawai mu dan huta. Ba mu taba tsammanin cewa zai iya zama da hadari haka ba. Yanzu saboda wannan abu da ya faru hankalinmu ya tashi," in ji Madhuparna Nandi, wata karamar likita mai neman kwarewa na kwalejin mai shekara 76, ta asibitin na Kolkata.
Yadda Dr Nandi ta kasance a wannan wajen aiki na nunawa a fili yadda mata lokitoci a asibitocin gwamnati ke hakuri da irin yanayin rashin tsaro da suke fuskanta.

A asibitin da take aiki, a matsayin likita mai neman kwarewa ta mata, babu wasu dakuna da aka ware na hutu ko kuma bandaki da aka ware na mata da na maza - duka daya ne.
Dr Nandi ta ce ''saboda haka nake amfani da bandakin marassa lafiya ko kuma na ma'aikatan jinya. Ida ina aikin dare nakan yi bacci a ganon marassa lafiya wanda ba kowa ko kuma a zaurn da masu neman ganin likita ke jira wanda ke cike da jama'a".
Ta ce hankalinta ba ya kwanciya hatta a dakin da take kwanciya ta huta bayan aikin kwana na sa'a 24, da take farawa da marassa lafiya na sha-ka-tafi da ci gaba da gewaya a dakunan marassa lafiya da kuma dakunan haihuwa.
Cikin wani dare a 2021 lokacin kamarin cutar Korona, wasu maza suka bankado cikin dakin da take suka tashe ta daga bacci ta hanyar taba ta, suna cewa, ''Tashi, tashi ki duba maras lafiyanmu.''
Hankalina ya tashi sosai da abin. To amma ba mu taba tunani abin zai kai ga yi wa likita fyade a kuma kashe ta ba a asibitin in ji Dr Nandi.

Abin da ya faru ranar Juma'a bva wai shi kadai ba ne.
Irin wannan abin wanda ya fi tayar da hankali shi ne na Aruna Shanbaug, wata ma'aikaciyar jinya a wani fitaccen asibiti a Mumbai, wadda wadda wani ma'aikaci ya bari rai kwakwai mutu kwakwai bayan ya yi mata fyade ya daure wuyanta a 1973.
Ta mutu a 2015, bayan shekara 42 tana fama da tsananin jinyar shanyewar wani bari na kwakwalwarta.
Haka kuma a kwanan nan a Kerala, wani maras lafiya da ya bugu da barasa, ya jiwa wata daliba likita mai koyon aiki, Vandana Das, mai shekara 23, mummuna rauni da almakashin tiyata a bara.
A asibitocin gwamnati da ke da jama'a da yawa inda kowa ke iya shiga ko'ina, likitoci kan fuskanci fushin dangin maras lafiya idan ya mutu ko kuma su nemi sai lalle likita ya kula da maras lafiyansu.
Kamna Kakkar, likita ce mai yin allurar rage radadi, ta tuna wani mummunan lamari inda wani lokaci da take aikin dare a shashen marassa lafiya da ke rai-kwa-kwai-mutu-kwa-kwai a lokacin annobar Korona a 2021 a asibitinta a Haryana da ke arewacin Indiya.
“Ni ce likita kwaya daya tilo a sashen a lokacin inda wasu maza uku suna kwarmata suna wani dan siyasa suka kutsu cikin sashen suna son lalle a ba su wani magani da ake matukar bukata - wanda ba a bayar da shi haka kawai. Ala dole na ba su domin na kare kaina, duk kuwa da sani cewa rayuwar marassa lafiyan da nake kula da su na cikin hadari, " in ji Dr Kakkar.
Namrata Mitra, wadda ke aiki a asibiti a Kolkata- wadda ta yi karatu a kwalejin kolyon aikin likita ta RG Kar Medical College, ta ce babanta likita yawanci shi yake raka ta aiki saboda hankalinta ba ya kwanciya idan ita kadai za ta.

“A lokacin aikina na dare, tare da babana muke tafiya. Ana min dariya, don ina kwanciya a wani daki mai kofar rodi, wadda ma'aikaciyar jinay ce kadai za ta iya bude dakin idan an kawo maras lafiya,'' kamar yadda Dr Mitra ta rubuta a shafinta na Facebook a karshen mako.
''Ba na jin kunya wai cwa ina jin tsoro . Idan kuma wani daga cikin dakin marassa lafiya, ma'aikacio ko ma maras lafiya ya nemi ya yi min wani abu? Ina amfani da damar cewa mahaifina likita ne, to amma ba kowa ba ne yake da wannan dama.''
Lokacin da take aiki a wata cibiyar kula da lafiya a gundumar West Bengal, Dr Mitra na kwana a wani gida maras kyau, mai bene daya da ke zaman wajen kwanan likitoci
“Haka cikin dare gungun yara maza zai taru a kusa da gidan, suna fadar maganganu na batsa yayin da muke shige da fice idan an kira mu aiki na gaggawa.
Sai su nemi mu gwada musu yanayin bugun jininsu don dai kawai su taba jikinmu. Kuma za ka ga har leke suke ta tagogin bandakin gidan,'' kamar yadda ta rubuta.
Bayan wasu shekaru, a lokacin wani aikin gaggawa da aka kira ni a wani asibitin gwamnati , gungun wasu maza da suka sha giya, ya wuce ni, har wani daga cikinsu ya nemi ya rike ni, in ji Dr Mitra. ''Da zan gaya wa wani dansanda sai na ga ashe ma bacci yake da bindigarsa kuma a hannu.”

Abubuwa sun kara tabarbarewa a cikin shekarun nan in ji Saraswati Datta Bodhak, likita a wani asibitin gwamnati a gundumar West Bengal.
"'Ya'yana mata biyu kananan likitoci ne, suna gaya min cewa bata-gari da sauran matasa 'yan bana-bakwai da 'yan giya kan mamaye wajen kwanan likitoci da ke asibitoci a jihar," in ji ta. Dr Bodhak tana iya tuna wani lokaci da wani mutum rike da bindiga yake yawo a cikin wani babban asibitin gwamnati a Kolkata lokacin wata ziyara.
India ba ta da wasu tsauraran dokoki na tarayya na kare ma'aikatan lafiya.
Kodayake jihohi 25 suna da wasu dokoki na kre aikata musu ta'addanci, amma kuma duk da haka kusan ba ka taba jin an yanke wa wani hukunci kan cin zarafin ma'aikan lafiya, kamar yadda wani likita na kungiyar likitoci ta India ya bayyana wa BBC.
Wani bincike ya nuna cewa kashi 75 cikin dari na likitoci a India ya taba fuskantar wani nau'i na cin zarafi a wajen aiki.
“Kusan ma babu tsaro a asibitoci,”ya ce. “Dalili kuwa shi ne ba wanda ma yake tunanin cewa asibiti waje ne na rikici.”
Wasu jihohi kamar Haryana sukan dauki jami'an tsaro masu zaman kansu domin karfafa tsaro a asibitocin gwamnati.
A 2022 gwamnatin tarayya ta bukaci jihohi da su dauki kwararrun jami'an tsaro a asibitocin da ke iya fuskantar matsalar tsaro, sannan su sanya na'urar daukan hoto ta tsaro, da sanya masu tsaro na kar-ta-kwana da takaita shiga ga bata-gari da kuma kai karar wadanda suka saba doka. To amma duk da wannan ba wani abu da ya taba faruwa karara.
Hatta su kansu likitocin masu korafi da nuna damuwa a kai ba su da kwarin gwiwa za a yi wani abu a kai.
Abin da suke gani zai ci gaba shi ne, ''likitoci su ci gaba da aiki ba dare ba rana su kuma jure cin zarafin da ake yi musu a matsayin al'ada kawai,'' in ji Dr Mitra. Abu ne mai karya gwiwa.