by MUHAMMAD AUWAL UMAR
July 25th 2024.

Wasu sojojin Najeriya sun koka kan rashin biyansu alawus

Christopher Musa

ASALIN HOTON,X/DEFENCE HQ

A Najeriya, wasu daga cikin sojojin kasar da ke ayyukan samar da tsaro a jihar Zamfara sun koka game da yawan jinkirin da ake samu, wajen biyansu kudadensu na alawus, inda suka ce akan biya su kudin wata guda ne kacal bayan kwashe watanni biyu ko uku, lamarin da ke jefa su cikin halin ƙaƙa-ni-ka-yi a cewarsu.

Sai dai hukumomin sojan Najeriyar sun ce suna sane da wannan kalubale da ke gaban dakarun da ke fagen daga, amma ana kokarin shawo kan lamarin nan ba da dadewa ba.

Wasu sojojin da suke aiki karkashin rundunar Operation Hadarin Daji a jihar ta Zamfara, ne suka shaida wa BBC korafin nasu.

Sun bayar da misali da cewa, sai a ranar Litinin ta wannan mako aka fara biyansu alawus na watan Mayun da ya gabata.

Har ma sun fara bayyana fargaba, cewa mai yiwuwa kafin a biya su alawus na watan Yuni sai cikin watan Satumba mai zuwa.

Sun ce akwai ma wadanda daga cikinsu har yanzu ba a ma biya su alawus na watan Maris ba.

Sojojin da ke fagen dagar sun bara, cewa tsaikon biyansu alawus na jefa su cikin tsaka-mai-wuya.

Dangane da wadannan korafe-korafe dai, BBC ta tuntubi Guruf Kyaftin Ibrahim Ali Bukar, mataimakin daraktan watsa labarai na hedikwatar tsaron Najeriyar, inda ya yaba da irin ƙoƙarin da dukkan jami'ansu suke yi wajen yaki da ƴan'ta'adda.

Sannan ya ce: "Shugaban sojoji Janar Christopher Musa, zai yi duk abin da zai yuwu domin ganin an kyautata masu, kuma su ci gaba da samun nasarori a daƙile ƴan ta'adda, dangane da matsaloli da ake fuskanta, ana kan yin abin da ya dace, da zaran babban bankin Najeriya ya kammala aikinsa kowa zai samu abinshi, Insha Allah."

Guruf Kyaftin Ibrahim Ali Bukar ya ce Janar Christopher Musa ya yi kwamandan yaƙi saboda haka ya san dukkan matsalolin da ke tattare da soja a daji, "Kowa zai samu kudinsa kai tsaye ta asusun bankinsa saboda haka ake yi."

Korafin na tsaikon biyan alawus ga dakarun Najeriya da ke fagen daga dai, ba wai a jihar Zamfara kadai ya tsaya ba, domin kuwa binciken da BBC ta gudanar ya nuna cewa, abin yana nema ya zama wani ruwan dare a kasar.

Al'amarin da masana harkokin tsaro ke ganin yana iya shafar karsashin dakarun, idan har ba a hanzarta yi wa tufkar matsalar hanci ba.

MUKHZAFAYA GLOBAL RAHAMANIYA ENTERPRISES user

MUHAMMAD AUWAL UMAR

[email protected]
Search Website

Search

Subscribe

Newsletter

WhatsApp Google Map

Safety and Abuse Reporting

Thanks for being awesome!

We appreciate you contacting us. Our support will get back in touch with you soon!

Have a great day!

Are you sure you want to report abuse against this website?

Please note that your query will be processed only if we find it relevant. Rest all requests will be ignored. If you need help with the website, please login to your dashboard and connect to support