Tareni: Yadda Sakkwatawa ke sarrafa naman layya

- Marubuci, Bashir Zubairu Ahmad
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News Hausa
- Aiko rahoto daga Sokoto
A ranar sallah bayan an sauko daga Idi, a bisa al'adar addinin Musulunci liman kan fara yanka dabbarsa ta layya kafin sauran jama'a su bi sahu.
A ƙasar Hausa akwai al'adu daban-daban na sarrafa naman layya. Wasu ɗanye su kan raba wa mabuƙata yayin da wasu kan dafa ko soya naman kafin su raba wa jama'a.
Amma a jihar Sokoto da ke arewa maso yammacin Najeriya, wannan al'ada ta sha bambam.
Bayan yanka dabbar layya tare da fyeɗe don fitar da kayan cikin gaba ɗaya, akan buɗe dabbar da aka yankan a tsaga kirjinta a wanke shi sarai, a saka masa itatuwan da za su banƙare shi, kamar dai gicciye, sannan a rataye kowane rago akan wani babban sanda da aka kafe a ƙasa, a tsari irin na hannun riga, a dai yi kamar da'ira sai a saka guma-gumai a tsakiya a kunna wuta.

Za a ci gaba da juya wutar sannu a hankali zafin harshen wuta da garwashi za su ci gaba da gasa naman har zuwa lokacin da aka tabbatar da gaban ya gasu sannan a juya bayan kowane rago domin ya sha wuta.
Wannan irin gashi shi ake kira "tareni". Kuma al'ada ce da ta keɓanta ga yankin Sokoto da kewaye, kamar Zamfara da Kebbi da wasu sannan Jamhuriyar Nijar.
To ko ya ake da naman bayan an gasa?
Idan an gasa naman ba ranar ake cin sa ba, akan ajiye shi ne sai ya kwana ɗaya sannan a raba wa mabuƙata da dangi da duk wanda rabonsa ya tsaga.
Amma sauran kayan cikin dabbobin tun a ranar salla ake soya su, sai dai wannan aikin na mata ne a gida.
Waɗanda ke samun taimakon yara wajen cire dattin kayan cikin tare da wankewa kafin a saka tukunya a fara suya.

Idan aka wanke su sai a soya domin fara ci tun a ranar, kuma daga somawa nan take za a ji ƙamshi ya game gari, har ta kai ma ana yi wa layya kirarin "kakar nama", domin kuwa ko mutum bai yi ba, zai wadata
Ina al'adar tareni ta samo asali?

Su wane ne ke gasa tareni?
A bisa al'ada mahauta ne ke wannan aiki, to sai dai zamani ya zo da mutane da dama da ba mahauta ba sukan tsunduma ciki.
Ba ma gashi irin na tare ni ba, yanzu fyede dabba ma a ranar layya za ka ga kusan kowa zai gwada tasa hikima, wannan kan kai ga huje fatar dabbar da aka fyeɗe aka bayar sadaka, ya sa ko dai ta lalace ga mai saye ko farashinta ya fadi.
Wasu dattawa da BBC ta tattauna da su, sun ce al’adar tareni ta kwashe shekaru ana yi, abin da suka bayyana da cewa tun bayan jihadin Shehu Usman Danfodiyo.
Da Musulunci ya ƙara wanzuwa aka ƙarfafa layya ake wannan al’adar a jihar Sokoto.
Wasu sun ce kasancewar Sokoto gari ne na karrama baki suke ganin a maimakon a bai wa mutum tsokar naman layya ɗanye guda ɗaya jal, sai a ba shi wanda aka gasa, wato dai daga buhu sai tukunya, a baki kawai zai saka an hutar da shi dafawa.
To sai dai zuwan sauyin zamani ya sa a yanzu ana samun wasu da suka soma karkata daga wannan al’ada da aka gada kaka da kakakkani, inda suke sare naman layyarsu tun yana ɗanye su aika gida.

Amma da yawa masu ra’ayin ƴan mazan jiya na kallon wannan a matsayin rowa domin kuwa ba kowa ne zai so a ba shi nama ɗanyensa ba, musamman idan ba shi da yawa.
To sai dai kuma wasu daga cikin masu wannan tsari na sarrafa nama danyensa na cewa suna ganin ya fi tsafta da hutar da mai layya.
A duk lokacin da ake wannan al’ada ta gasa tareni, ‘yan uwa da maƙwabta kan taru wuri ɗaya, a ci abinci a kuma yi aiki tare, abin da ake ganin wata hikima ce ta riƙe da ɗorewar zumunta.